Alkali Mai Ritaya Ya Caccaki CJN Kan Rashin Wakilcin Wasu Yankuna a Alkalan Kotun Koli
- Alƙalin kotun ƙoli, mai shari'a Dattijo Muhammad, ya bayyana damuwarsa kan yadda aka yi watsi da yankuna biyu na ƙasar nan a cikin alƙalan ɗaukaka ƙara na zaɓen shugaban ƙasa
- Ya soki alƙalin alƙalan Najeriya (CJN), mai shari'a Kayode Ariwoola, kan yadda ya kasa gudanar da aikinsa bisa gaskiya
- Ya bayyana damuwarsa ne a taron tabbatar da ritayarsa domin kawo ƙarshen shekaru 43 da ya yi a fannin shari'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Alƙalin kotun ƙoli mai ritaya, Dattijo Muhammad, ya yi kakkausar suka ga ƙarfin ikon da ya wuce ƙima da alƙalin alƙalan Najeriya (CJN) ke rike da shi, tare da bayyana damuwarsa kan yadda aka kafa kwamitin alƙalan sauraron ɗaukaka ƙarar zaɓen shugaban ƙasa.
Mai shari'a Muhammad, wanda ya cika shekara 70 na yin ritayar dole, ya bayyana haka ne a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba, a wani zama da aka yi na karrama shi a harabar kotun ƙoli da ke Abuja, kamar yadda Premium Times ta rahoto.
A wani mataki da ba a taɓa ganin irinsa ba, mai shari’a Muhammad ya fito fili ya nuna shakku kan yadda ake ta'ammali da madafun iko a cikin ma'aikatun shari'ar ƙasar nan wanda CJN mai ci ke mora.
Ku tuna cewa CJN mai ci a yanzu Olukayode Ariwoola ba ya cikin alƙalan da suka yanke hukunci kan ƙarar zaɓen shugaban ƙasa, amma shi kaɗai ke da alhakin kafa kwamitin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai shari'a Muhammad, wanda ya yi aikin shari’a na tsawon shekaru 43, ya yi nuni da cewa, ritayar tasa ta rage adadin alƙalan kotun ƙoli zuwa 10, lamarin da ya sa yankuna biyu na kasar ba su da wakilci.
Alƙali mai murabus ya nuna damuwa kan rashin wakilcin yankuna biyu
A rahoton Channels TV, ya kuma nuna damuwarsa kan yadda aka zaɓo alƙalan guda bakwai da suka yi watsi da ƙarar da Atiku Abubakar da Peter Obi suka shigar kan zaɓen Shugaba Tinubu, inda ya jaddada cewa ya kamata a samu wakilcin dukkanin yankunan ƙasar nan guda shida.
Mai shari'a Muhammad ya yi nuni da cewa rage adadin alƙalan kotun ƙoli da aka yi an yi shi ne da gangan.
Sai dai, CJN Olukayode Ariwoola ya bayar da tabbacin cewa ana ƙoƙarin naɗa ƙarin alƙalai a kotun ƙoli.
Falana Ya Magantu Kan Hukuncin Kotun Koli
A wani labarin kuma, fitaccen lauya mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana ya yi tsokaci kan hukuncin da kotun ƙoli ta yanke kan ɗaukaka ƙarar da ke ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu.
Femi Falana ya yi nuni da cewa ko kaɗan bai kamata a ce kotun ƙoli ba ce za ta warware taƙaddamar zaɓen Najeriya.
Asali: Legit.ng