Tunji Olaopa: Muhimman Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban FCSC

Tunji Olaopa: Muhimman Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban FCSC

FCT, Abuja - An nada Tunji Olaopa a matsayin sabon shugaban hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya (FCSC) a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Olaopa tare da wasu mutum 11 domin jagorantar al’amuran ma’aikatan kasar.

Shugaban hukumar FCSC, Tunji Olaopa
Tunji Olaopa: Muhimman Abubuwa 10 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban FCSC Hoto: @Soy_Florens
Asali: Twitter

Sai dai kuma, majalisar dattawa ce za ta tabbatar da Olaopa a kan wannan mukami.

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da sabon shugaban na FCSC, Tunji Olaopa, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.

  1. An haifi Olaopa wanda ya fito daga Aáwé, jihar Oyo a ranar 20 ga watan Disambar 1959.
  2. Sabon shugaban na FCSC ya mallaki digiri a bangaren kimiyyar siyasa a 1984 da kuma digiri na biyu a 1987 daga jami'ar Ibadan. A 2006, ya samu digiri na uku a fannin Gudanar da harkokin Jama'a daga Jami'ar Commonwealth, kasar Birtaniya.
  3. Ya kasance gogaggen masanin yadda ake tafiyar da harkokin jama'a, masanin kimiyyar siyasa kuma Mawallafi.
  4. Olaopa ya yi aiki a matsayin babban jami'in bincike, mai nazarin manufofi kuma marubuci a fadar gwamnati, Abuja, a 1988.
  5. Haifaffen dan jihar Oyon ya kuma kasance jagoran binciken bangaren Ilimi kuma shugaban sashen manufofi, Ofishin Minista a Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya.
  6. Ya kasance daraktan shirye-shirye, Ofishin gyaran ma'aikata na gwamnati.
  7. Olaopa ya kuma rike mukamin mataimaki na musamman ga shugaban ma'aikatan Najeriya kan gyare-gyaren ma'aikatan gwamnati.
  8. Ya kasance darakta a ma'aikatu, sassan da hukumomin gwamnati.
  9. Olaopa shi ne ya kafa makarantar gwamnati da manufofin jama'a ta Ibadan wato ISGPP.
  10. Ya samu lambar yabo ta kasa a shekarar 2015, da kuma lambar yabo ta Thabo Mbeki a shekarar 2018.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Ya Yi Manyan Nade-Nade 12 a Hukumar Kula Da Ma’aikatan Tarayya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya nada shugaban hukumar FCSC

A baya Legit Hausa ta rahoto cewa mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, ne ya sanar da batun nadin Olaopa a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoba.

Ngelale ya bayyana cewa shugaban kasar ya yi nadin ne bisa karfin ikon da sashi na 154 na kundin tsarin mulkin Najeriya (kamar yadda aka gyara) ya ba shi.

Ya kuma bayyana cewa ana jiran majalisar dattawa ta tantance tare da tabbatar da wadanda aka nada kan mukaman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng