Alkalin Kotun Koli Musa Dattijo Ya Yi Ritaya Daga Alkalanci
- Mai shari'a Musa Dattijo, Alkalin kotun koli, zai yi ritaya a ranar 27 ga watan Oktoba kamar yadda mai magana da yawun kotun kolin, Festus Akande ya sanar
- Za a yi zama na bankwana don karrama shi karkashin jagorancin Alkalin Alkalai na Najeriya Olukayode Ariwoola a babban dakin shari'a na kotun koli
- Ritayar da Dattijo ya yi ya rage adadin alkalan kotun zuwa 10, hakan na nufin akwai gibin 11 idan aka yi la'akari da adadin 21 da kundin mulkin kasa na 1999 ya tanada
FCT, Abuja - Musa Dattijo, Alkalin kotun koli, zai yi murabus, a hukumance daga alkalanci a ranar Juma'a, 27 ga watan Oktoban 2023.
An bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kotun kolin, Festus Akande, ya fitar a ranar Lahadi, 22 ga watan Oktoba.
Legit Hausa ta tattaro cewa za a shirya zaman bankwana don karrama alkalin da zai yi ritaya a ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
The Punch ta rahoto cewa ritayar na Dattijo ne zuwa ne bayan ritayar Aminu Augie a watan Satumban 2023, da kuma rasuwar Mai shari'a Chima Nweze a Yulin shekarar ta 2023.
Da wannan cigaban, adadin alkalan kotun kolin ya zama 10, akwai gibin 11 don cika 21 kamar yadda sashi na 230 (2) na kundin tsarin mulkin kasa na 2023.
CJN Ariwoola zai jagoranci zaman karramawa a kotun
Akande ya ce Alkalin Alkalai na Najeriya, Olukayode Ariwoola, zai jagoranci zama na musamman da za a yi don karrama Mai Shari'a Dattijo tare da sauran manyan masu ruwa da tsari a bangaren shari'a na kasar.
Za a yi taron ne a babban dakin sauraron shari'a na kotun koli ta Najeriya da ke birnin tarayya a Abuja.
Wanene Mai Shari'a Musa Dattijo?
An haife Mai Shari'a Musa Dattijo ne a Minna, babban birnin jihar Neja a ranar 27 ga watan Oktoban 1953. Asalinsa dan karamar hukumar Chanchaga ne.
Ya zama alkalin kotun koli a ranar 10 ga watan Yulin 2012.
Alkalin kotun da ke shirin ritaya ya samu karin girma daga Kotun Daukaka Kara ne a ranar 21 ga watan Nuwamba, daga Ma'aikatar Shari'a na Jihar Neja, inda ya yi ayyuka a sassa daban-daban tare da nuna hazaka.
Mai shari'ar ya fara karatunsa a Native Authority School, Minna, daga 1960 -1966; ya yi sakandare a Kwalejin Sheikh Sabbah (yanzu Kwalejin Tunawa da Sardauna) a Kaduna daga 1967 - 1971, sannan ya tafi Kwalejin Abdullahi Bayero (yanzu Jami'ar Bayero) Kano daga 1972 - 1973 inda ya yi satifiket na kafin digiri.
Ya yi digiri dinsa a bangaren Shari'a a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria daga 1973 - 1976 sannan ya tafi Makarantar Horas da Lauyoyi a 1977. Ya kuma tafi Jami'ar Warwick a Birtaniya don yin digiri na biyu (LLM) daga 1982 - 1983, kuma ya halarci Cibiyar Zurfafa iya Aikin Shari'a.
Asali: Legit.ng