Hambararren Shugaban Kasar Nijar Ya Yi Yunkurin Tsere Wa Daga Hannun Sojoji

Hambararren Shugaban Kasar Nijar Ya Yi Yunkurin Tsere Wa Daga Hannun Sojoji

  • Mohammed Bazoum, shugaban Jamhuriyar Nijar da aka hamɓarar ya yi yunkurin tserewa daga hannun sojoji
  • Kakakin gwamnatim soji, Amadou Abdramane ne ya bayyana haka yana mai cewa an dakile shirin kuma an kama masu hannu
  • Tun da sojoji suka kifar da gwamnatinsa a watan Yuli, Bazoum ya ƙi yarda ya yi murabus a hukumance

Tsohon shugaban Nijar da aka hamɓarar daga kan madafun iko, Mohamed Bazoum, ya yi yunkurin tsere wa daga inda sojoji ke tsare da shi ranar Alhamis.

Sojojin da suka kifar da gwamnatin Bazoum a watan Yulin da ya gabata ne suka bayyana haka, amma sun ce sun daƙile yunƙurin cikin nasara.

Hambararren Shugaban Nijar, Mohamed Bazoum.
Sojoji sun dakile yunkurin Bazoum na guduwa zuwa Najeriya Hoto: channelstv
Asali: UGC

Channels tv ta tattaro cewa kakakin gwamnatin sojin Nijar, Amadou Abdramane, a wani jawabi da ya yi a gidan talabijin, ya ce:

"Da misalin karfe uku na safe, hambararren shugaban kasa, Mohamed Bazoum da iyalansa, da masu dafa masa abinci guda biyu, da dogaransa biyu sun yi kokarin tserewa daga inda ake tsare da shi."

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Waiwayi Leburori, Ya Ce Zai Ɗauki Nauyin Karatunsu Har Su Gama Jami'a Bisa Sharaɗi 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ƙara da cewa yunƙurin da suka yi bai kai ga nasara kuma tuni dakarun soji suka damƙe waɗanda suka ƙulla guduwar da sauran waɗan da ke da hannu a lamarin.

A halin yanzun Gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar ta fara gudanar da bincike kan wannan lamarin.

Yadda Bazoum ya yi ƙoƙarin guduwa Najeriya

"A tsarin da suka yi na guduwar Bazoum, a matakin farko zai tsere ne zuwa wata maɓoya a wajen babban birnin ƙasar," in ji Abdramane.

Ya kara da cewa, sun yi shirin tashi a jirage masu saukar ungulu "na wata kasar waje" zuwa Najeriya, in ji shi, inda ya yi tir da halin rashin da'a na Bazoum.

Tun da sojoji suka kifar da gwamnatinsa ranar 26 ga watan Yuli, 2023, Bazoum ya ƙi yarda ya yi murabus daga kujerar shugaban ƙasa a hukumance.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Sanya Ranar Yanke Hukunce Kan Sojojin da Suka Halaka Sheikh Goni Aisami

Har ya zuwa yanzu, yana tsare a gidansa da ke tsakiyar fadar shugaban kasa, tare da matarsa ​​Haziza da dansa Salem, The Guardian ta ruwaito.

Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kebbi da Wasu 12

A wani rahoton kuma 'Yan bindiga sun tare wata motar haya, sun sace tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kebbi da wasu mutane 12.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun tare motar, wacce ta taso daga Abuja a kan titin Tegina zuwa Kontagora.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262