Zulum Ya Sa a Rushe Gidajen Magajiya a Kwace Filayensu a Maiduguri
- Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum ya ba da awanni 72 a rusa gidajen karuwai da matattarar bata-gari a Maiduguri
- Zulum ya ba gidajen karuwan awanni 12 kowa ya kama gabansa tare da kwace filayensu wanda gwamnati ta bai wa hukumar jiragen kasa
- Gwamnan ya ce wadannan miyagun ayyukan na barazana ga zaman lafiya da kuma tarbiyya a cikin al’umma
Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya bayar da umurnin rushe gidajen karuwai da sauran wuraren da ake aikata badala a garin Maiduguri, babban birnin jihar.
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Gwamna Zulum ya bayar da wannan umurnin ne a ranar Talata, 17 ga watan Oktoba.
Ya ba da umurnin ne yayin wata ziyara da ya kai daya daga cikin irin wadannan wurare a ‘Bayan Quarters’, wani unguwa da ke kusa da gidajen ma'aikatan layin dogo.
Gwamnatin Borno ta ba da awanni 72 a rusa gidajen karuwai
Yankin na kunshe da yan daba, masu aikata laifuka sannan kuma ana amfani da kananan yara don aikin karuwanci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya nuna damuwarsa kan hauhawan miyagun laifuka da ke da alaka da gidajen karuwai, da kuma mabuyar masu laifi da suka hada da karuwanci, safarar miyagun kwayoyi da sauran ayyukan assha.
Ya yi nuni da cewa,wadannan ayyukan na kawo barazana ga tsaro domin yan iska na ci gaba da dagula al’amuran zamantakewa da ke kawo cikas ga rayuwar al’umma da mutuncin mutane.
Zulum ya yi bayanin cewa yayin da za a rushe gidajen da ke tattara masu aikata laifuka da yin lalata da kananan yara mata a cikin sa’o’i 72, su kuma gidajen karuwai an basu sa’o’i 12 su bar wajen.
Zulum ya kuma sanar da soke takardar mallakar fili inda ake ci gaba da aikata irin wadannan laifuka, wanda ya ce tun da farko hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya ta amince da amfani da shi.
Ya kuma bayyana kwace filayen da ake aikata wadannan aika-aikan wanda da farko aka bai hukumar jiragen kasar.
Ya ce kwace filayen ya zama dole, ganin yadda hukumar jiragen kasar ke ba da hayar filayen ga masu aikata laifi da tattara bata-gari, rahoton Aminiya.
Yan Gidan Magajiya Sun Harzuka Sun Maka Kwastoma A Kotu Kan Tura Musu Alat Na Bogi Bayan Sun Gama Harka
A wani labarin, an gurfanar da wani matashi mai suna Oluwafemi Damilola a gaban kotun Magistare da ke jihar Ondo bisa zargin kin biyan wasu mata hakkinsu bayan ya kwana da su har N45,000.
Wanda ake zargin ya damfari mata guda huɗu masu suna Glory David da Akere Bright da Valria Isaac da kuma Ngozi Okoro yayin da ya tura musu sakon banki na karya.
Asali: Legit.ng