Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'adda 50, Sun Kama 114 Cikin Mako Daya a Arewa

Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'adda 50, Sun Kama 114 Cikin Mako Daya a Arewa

  • Gwarazan dakarun sojin Najeriya sun halaka gwamman 'yan ta'adda a shiyyoyin arewa uku cikin mako ɗaya
  • Hedikwatar tsaro ta ƙasa ta bayyana cewa akalla 'yan ta'adda 50 ne suka sheƙa barzahu yayin da sojojin suka ceto mutane 49
  • Ta ce a tsawon mako ɗaya, sojojin sun kama yan ta'adda sama da 100, yayin da wasu suka miƙa wuya a Yobe da Borno

FCT Abuja - Hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta sanar da cewa dakarun sojoji sun kashe 'yan ta'adda 50 tare da kama wasu 114 cikin mako guda.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, DHQ ta ce sojin sun samu nasara ne a ayyuka daban-daban da suka gudanar a Arewa maso Gabas, Arewa ta Tsakiya da Arewa maso yamma.

Dakarun sojin Najeriya sun kashe yan ta'adda.
Sojoji Sun Halaka 'Yan Ta'adda 50, Sun Kama 114 Cikin Mako Daya a Arewa Hoto: HQNigerianArmy
Asali: Facebook

Daraktan yaɗa labarai na Hedkwatar tsaro ta ƙasa, Manjo Janar Edward Buba, shi ne ya faɗi haka yayin da yake jawabi ga 'yan jarida ranar Alhamis a Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wasu Garuruwa, Sun Halaka Babban Basarake a Jihar Arewa

Buba ya ce sojojin sun kuma ceto mutane 49 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda, kamar yadda Channels tv ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Arewa maso Gabas

Ya ce rundunar Operation Hadin Kai da ke Arewa maso Gabas ta ci gaba da matsa wa ‘yan ta’addan Boko Haram da ISWAP, wanda ya tilasta wa wasu mayaƙa miƙa wuya a Yobe da Borno.

A cewarsa dakarun sojin sun kuma kwato makamai da suka haɗa da bindigogi ƙirar AK47 18, alburusai 137 da wayoyin hannu guda biyu.

"Sojojin sun kuma kashe 'yan ta'adda 12, sun kama 26 tare da kubutar da wasu mutane shida da aka yi garkuwa da su a yankin Arewa maso Gabas," in ji shi.

Arewa ta Tsakiya

Buba ya ce dakarun Operation Safe Haven da ke Arewa ta tsakiya sun cafke masu garkuwa da mutane ne a kananan hukumomin Kanam da Sanga na jihohin Filato da Kaduna.

Kara karanta wannan

Babban Hafsan Tsaron Najeriya Ya Dira Jihar Arewa, Ya Aike da Kakkausan Saƙo Ga Yan Ta'adda, Ya Ba Su Zaɓi 2

Ya ce dakarun sojin sun sheƙe yan ta'adda 2, suka kamo wasu 12, kana suka ceto mutane uku da aka yi garkuwa da su. Sannan sun kwato makamai da kayan aiki.

“Jimulla, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda hudu, sun kama wasu 28 tare da kubutar da mutum biyu da aka yi garkuwa da su a Arewa ta Tsakiya."

Arewa maso Yamma

A yankin Arewa maso Yamma, Buba ya ce dakarun Operation Hadarin Daji sun kai same tare da sheƙe ‘yan ta’adda a jihohin Katsina, Kaduna da Zamfara.

Kakakin DHQ ya ce a wani luguden wuta ta sama da aka yi a sansanin ɗan ta’adda, Kamilu Buzaru, a karamar hukumar Safana ta jihar Katsina, an yi nasarar kashe wasu da dama daga cikin ‘yan ta’addan.

'Yan Bindiga Sun Gindaya Sharaɗi Kafin Su Sako Ɗalibai Mata da Suka Sace a Jami'ar Arewa

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun turo saƙon kuɗin fansar da su ke buƙatar a biya gabanin su sako ɗaiban jami'ar jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Sabon Nadin Mukami Mai Muhimmanci a Hukumar FCTA

A ranar Litinin da daddare, masu garkuwan suka yi awon gaba da ɗalibai mata huɗu a gidajensu na wajen makaranta a Keffi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262