“Tinubu Ya Kirkiri Takardun Karatun Da Ya Gabatarwa INEC Ne”: Lauyan Atiku
- Har yanzu Atiku Abubakar na PDP na ci gaba da fafatawa da Bola Tinubu a kokarinsa na neman adalci a kotu
- A ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba, dan takarar na PDP ya yi jawabi a taron manema labarai inda ya tattauna batutuwa kan zaben 2023 da abubuwan da ya gano a jami'ar Chicago
- Sai dai kuma, lauyan Atiku ya bayyana wasu abubuwa masu ban al'ajabi kan takardun da shugaban kasar ya gabatarwa INEC a zaben 2023
FCT, Abuja - Wani lauyan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya yi sabbin zarge-zarge kan shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba, lauyan Atiku ya zargi shugaban kasa Tinubu da gabatarwa hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da takardun karatu na bogi gabannin zaben 2023.
Channels TV ta rahoto cewa lauyan, Kalu Kalu, ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da Atiku ya kira bayan jami'ar jihar Chicago ta sanar masa takardun karatun shugaban kasar.
Koda dai Tinubu da magoya bayansa sun karyata zargin kirkirar takardun, Mista Kalu ya yi bayanin cewa takardar da aka saki ya tabbatar da badakalar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da aka tambaye shi game da abun da takardun suka nuna ya ce:
"Daya, cewa Bola Ahmed Tinubu ya kirkiri takardar da ya gabatarwa INEC.
"Wannan takardar ta nuna cewa mamallakin takardar bakin Ba'amurke ne kuma a takardar da Bola Ahmed Tinubu ya gabatarwa INEC, ya karyata cewar ya mallaki katin shaidar zama dan kasa guda biyu wanda hakan ke nufin ba na shi bane. Sannan kuma, wannan takardar ya nuna, bayanin fatar baki, ya ce A da ke cikin Bola A Tinubu, Ahmed ne amma satifiket din NYSC da Bola Ahmed Tinubu ya gabatarwa INEC yana dauke daAdekunle. Ban san daga ina Adekunle ya fito ba."
Atiku ya yi kira ga Kwankwaso da Peter Obi su hada kai da shi don cire Tinubu, ya bada dalili
A gefe guda, Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben ranar 25 ga watan Fabrairu, ya yi kira ga takwarorinsa na jam'iyyar Labour da NNPP, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso su hada kai da shi a kokarinsa na korar Tinubu daga kujerar shugaban kasa.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi wannan kiran ne yayin jawabinsa na kai tsaye da wakilin Legit Hausa ya bibiya a ranar Alhamis, 5 ga watan Oktoba, game da abubuwan da suka bayyana a baya-bayan nan kan takardun Tinubu a Jami'ar Jihar Chicago, CSU.
Asali: Legit.ng