EFCC: An Cafke Mutumin Jonathan da Orubebe, An Yanke Masu Daurin Shekaru 6

EFCC: An Cafke Mutumin Jonathan da Orubebe, An Yanke Masu Daurin Shekaru 6

  • Kotun tarayya ta samu George Turnah da wasu kamfanoni da laifuffukan da su ka shafi satar kudi
  • A karshen zaman da aka yi a Fatakwal, hukumar EFCC ta yi galaba a kan tsofaffin jami’an gwamnati
  • George Turnah ya na da kusanci da Goodluck Jonathan, ya taba zama hadimi na musamman a NDDC

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - Alkalin kotun tarayya da ke zama a Fatakwal a jihar Ribas, A. T. Mohammed, ya zartar da hukuncin dauri a kan su George Turnah.

Hukumar EFCC ta sanar a shafinta na yanar gizo cewa kotu ta daure mai ba tsohon hukumar NDDC, Mista Dan Abia shawara na musamman.

George Turnah da Ebis Orubebe da kuma Uzorgor Silas Chidebere sun samu daurin shekaru shida bayan samunsu da laifi da su ka shafi sata.

EFCC.
EFCC ta aika wasu gidan yari Hoto:Getty Images
Asali: Getty Images

Hukumar EFCC ta yi nasara a kotu

Kara karanta wannan

Ga ci ga rashi: An kwace kujerar sanatan PDP a Arewa, an ba wani fitaccen tsohon gwamnan APC

Alkalin kotun na Fatakwal ya ce an samu wadanda ake zargi da karya, laifin manyan sata, safarar kudi da canjinsu ta hanyar da ba ta dace ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mai shari’a A. T. Mohammed yake cewa an samu wadanda ake tuhuma da laifi a hukuncin da kotu ta zartar a ranar 7 ga watan Satumba 2023.

The Guardian ta ce an fara shigar da karar ne Mayun 2017, sai aka sake komawa kotu a watan Junairun 2023 bisa zargin aikata laifuffuka 23 a doka.

Lauyoyin hukumar EFCC sun gamsar da kotu cewa an samu wadanda ake kara a kotu da laifin wawurar N2, 894, 500, 000 daga lalitar gwamnati.

Kamfanoni sun shiga cikin matsala

Kamfanoin El-Godams Global Services Ltd., Turnoil and Gas Nigeria Ltd, Kolo Creek Petroleum Dev. Ltd, su na cikin wadanda aka yi kara a kotun.

Kara karanta wannan

An kuma: Sanatan APC ya yi nasara kan PDP a gaban kotu, an yi watsi da duk wani zargi

Sai Celtic Pride Consult & Events Ltd, Yenagoa Mall Ltd, The Incorporated Trustees of Concerned Niger Delta Initiative, da Adaka Boro Marine Services.

Ragowar su ne kamfanonin Sugarland Integrated Farms Nig. Ltd, Geohan Telecommunication Nig. Ltd, Daily Trust ta kawo rahoton yau.

EFCC ta ce George Turnah ya karbi dala $1000,000.00 a 2014, sai ya canza su ta hannun kamfanin Hakuri Global Concept, hakan ya saba doka.

Rikicin gidan PDP a Najeriya

An rahoto Pedro Obaseki ya na cewa Ministan birnin Abuja, Nyesom Wike ya na so ya rugurguza Jam’iyyar PDP saboda ya samu yin takara a 2027.

A cewar Obaseki, Wike ya ci amanar Rotimi Amaechi, Goodluck Jonathan, Peter Odili, da Atiku Abubakar, yanzu ya koma wajen Bola Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng