Tinubu Ya Shilla Zuwa Dubai Daga Indiya, Zai Gana Da Shugabannin Kasar

Tinubu Ya Shilla Zuwa Dubai Daga Indiya, Zai Gana Da Shugabannin Kasar

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gana da shugabannin haɗaɗɗiyar daular Larabawa (UAE) bayan taraon G-20 a Indiya
  • Shugaban ƙasa ya bi sahun shugabannin duniya a taron G-20 wajen kiran da a haɗa kai domin a magance matsalolin da suka addabi duniyar nan
  • Kakakin shugaban ƙasa Tinubu, Ajuri Ngelale, ya sanar da cewa Tinubu zai gana da shugabannin UAE a birni Abu Dhabi

Abu Dhabi, UAE - Shugaban ƙasa Bola Tinubu zai gana da shugabannin haɗaɗɗiyar daular Larabawa (UAE) a yayin wani yada zangon da zai yi a birnin Abu Dhabi na na ƙasar ta UAE.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa za a gudanar da ganawar ne domin warware matsalolin diflomasiyya da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Tinubu ya shilla zuwa Dubai
Tinubu zai tattauna da shugabannin UAE Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Matsalolin sun haɗa da hana biza da ƙasar ta sanya akan ƴan Najeriya tun watan Oktoban 2022 da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na Emirates zuwa Najeriya.

Kara karanta wannan

Jigon APC Ya Bayyana Muhimmin Dalili 1 Da Yakamata Atiku/Peter Obi Su Amince Da Hukuncin Kotu

Tinubu zai gana da shugabannin UAE

Hakan na zuwa ne bayan Shugaba Tinubu ya bar birnin New Delhi na Indiya, inda ya halarci taron G-20.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A cewar wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasan, Ajuri Ngelale ya fitar, tattaunawar ta Abu Dhabi za ta zama cigaba ne kan wacce shugabannin suka fara a baya.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Tattaunawar za ta magance matsaloli na musamman a dangantakar ƙasashen biyu bayan sun tattauna lokacin da jakadan UAE ya ziyarce shi a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
"Shugaban ƙasan zai warware matsalolin diflomasiyya da suka ƙi ci suka ƙi cinyewa a yayin yada zangon, sannan zai yi amfana da damar wajen ƙara tallata manufarsa ta nemo masu zuba hannun jari daga ƙasar."

Legit.ng ta rahoto cewa shugaban ƙasan zai dawo gida Najeriya yana kammala tattaunawa da shugabannin na UAE.

Kara karanta wannan

Kashim Shettima Ya Bayyana Yankunan Da Za Su Ci Gajiyar Mulkin Shugaba Tinubu

Osinbajo Ya Taya Tinubu Murnar Nasara a Kotu

A wani labarin na daban, tsohon mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya taya Shugaba Tinubu da mataimakinsa, Kashim Shettima kan hukuncin kotun zabe.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa wannan nasara a kotun sauraran kararrakin zaɓen shugaban kasa ta nuna tabbacin karfin dimukradiyya a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Tags: