Ministan Buhari Ya Bayyana Yadda Ya Yi Kwamishina Da Minista Ba Tare Da NYSC Ba

Ministan Buhari Ya Bayyana Yadda Ya Yi Kwamishina Da Minista Ba Tare Da NYSC Ba

  • Tsohon ministan sadarwa, Adebayo Shittu ya yi magana kan taƙaddamar NYSC ta ministar Shugaba Bola Tinubu
  • A cikin wata hira Shittu ya bayyana cewa Hannatu Musa Musawa ba ta da wani laifin da za a tuhumeta sannan batun baya da wani amfani
  • Ɗan siyasar wanda ya bayyana batun na Hannatu a matsayin mara amfani, ya ce kundin tsarin mulkin 1999 bai wajabta dole sai masu riƙe da muƙamai sun samu NYSC satifiket ba

Barr. Adebayo Shittu, tsohon ministan watsa labarai kuma jigo a jam'iyyar APC, ya yi magana kan cece-kucen da ake yi kan naɗa Hannatu Musa Musawa minista ba tare da ta kammala bautar ƙasa ba.

A wata tattaunawa da Daily Trust a ranar Asabar, 2 ga watan Satumba, ya bayyana cewa masu ɓata lokacinsu kan lamarin ba su san abin da doka ta ce ba ne.

Kara karanta wannan

Muje Zuwa: Shehu Sani Ya Bayyana Jam'iyyar Da Za Ta Ci Ribar Rikicin Siyasar Da Ke Tsakanin Gwamnan PDP Da Mataimakinsa

Adebayo Shittu ya magantu kan takaddamar NYSC
Tsohon minista ya ce batun NYSC na Hannatu Musa Musawa bai da amfani Hoto: Barrister Adebayo Shittu, Hannatu Musawa
Asali: Facebook

Tsohon ministan wanda ya yi fatali da taƙaddamar NYSC ɗin Hannatu, ya bayyana cewa:

"Ni a wajena wannan ba wani abun tayar da jijiyar wuya ba ne. A ƙasar nan muna bin tsarin kundin mulki na shekarar 1999."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Kundin tsarin mulkin 1999 bai wajabta dole sai wanda zai riƙe muƙamin siyasa yana da satifiket na NYSC ba."

Barr. Shittu ya bayyana yadda ya yi aiki a gwamnati, a matsayin ɗan majalisa a shekarar 1979, jim kaɗan bayan ya kammala makarantar lauyoyi.

A kalamansa:

"A shekarar 1979, na yi takarar kujerar ɗan majalisa a majalisar dokokin jihar Oyo, ina gama makarantar lauyoyi na yi takara a lokacin."
"Bari na fadi cewa ban yi bautar ƙasa ba. Na je na yi hidimar da ta fi wannan a majalisar dokokin jihar Oyo, sannan abokin takarata da na kayar na jam'iyyar NPN, ya kai ni ƙara kotu, amma kotu ta yi watsi da ƙarar. Ya ce kotu ta soke nasara ta saboda ban yi NYSC ba."

Kara karanta wannan

Bayan Juyin Mulkin Gabon, Shugaba Tinubu Ya Faɗi Ainihin Abinda Yake Jin Tsoron Ya Faru

"Duk da cewa lokacin daga makarantar lauyoyi na fito, kotun ta tambaya cewa a ina a cikin kundin tsarin mulki na 1979 aka ce idan za ka yi takara dole sai kana da satifiket ɗin NYSC."
"A lokacin da na gama aikina a majalisar dokoki na kai shekara 30, sannan aka naɗa ni kwamishinan cikin gida, watsa labarai da al'ada. Wannan a shekarar 1993 kenan, a lokacin ina da shekara 30."
"Abin da zan ce shi ne wannan ba magana ba ce mai amfani. Shugaban ƙasa yana buƙatarta a matsayi wanda ya wuce na NYSC. Zaɓin shugaban ƙasar ne ba ita ta naɗa kanta minista ba."

Tsohon Sanata Ya Caccaki Atiku

A wani labarin kuma, tsohon sanatan Oyo ta Kudu ya caccaki Atiku Abubakar kan ƙalubalantar nasarar Shugaba Tinubu a kotu.

Rilwan Soji Akanbi ya bayyana cewa bai kamata Atiku ya manta da abokantar da ke tsakaninsa da Tinubu ba, ya riƙa neman hanyar da zai ɓata masa suna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng