An Kama Tubabbun Yan Boko Haram 3 a Hanyarsu Ta Zuwa Sambisa Don Kai Wa Yan Ta’adda Kayan Amfani
- Wasu tubabbun yan ta'addan Boko Haram sun shiga hannu a hanyarsu ta zuwa dajin Sambisa
- Tsoffin mayakan da aka mayar garin Bama suna kai wa yan Boko Haram kayayyakin amfani a kauyen Barraram
- Wannan ba shine karo na farko da ake kama tubabbun yan ta'addan suna hada kai da miyagu ba a garin Bama
Jihar Borno - Wasu tubabbun yan Boko Haram da aka mayar garin Bama da ke jihar Borno sun sake shiga hannu kan zargin hada kai da yan ta'adda.
Kamar yadda shafin Zagazola Makama ya rahoto, an kama su ne tare da wasu mutane biyu a hanyarsa ta zuwa dajin Sambisa don haduwa da yan kungiyar ta'addancin.
An kama su a hanyar kai wa yan ta'adda kayayyakin amfani
An tattaro cewa suna kokarin kai wa mayakan kungiyar ta'addancin kayayyakin amfani a kauyen Barraram wanda aka fi sani da Daula Merket lokacin da suka shiga hannu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tubabbabun yan ta'addan uku da ke zaune a garin Bama suna ta taimakawa yan Boko Haram da kayayyakin amfani kamar su abinci, man fetur, tib da tayoyin babura da sauran kayayyakin amfani.
Garin Bama ya fuskanci irin wadannan lamura da dama na tubabbun yan ta'adda da ke hada kai da masu tayar da kayar baya wajen farmakan dakarun sojojin Najeriya.
Jama'a sun yi martani
@ahmed_shehu7 ya yi martani:
"Idan muka ce wadannan mutanen ba za su tuba ba sai mutane su ta fadin sabanin haka, duk wani dan ta'adda da aka kama a hukunta shi ba tare da bata lokaci ba."
@AyanniyiNoah ya ce:
"Lallai su tubabbu ne. Mutanen da ya kamata su je su tuba a gaban ubangijinsu."
@Austyn_reingz ya yi martani:
"Ku aika su gaban Allah ba tare da bata lokaci ba."
@umemuoo ya ce:
"Basu gama tuba ba kenan. Ku kara masu lokaci su tuba da kyau."
@Jameeelmb ya yi martani:
"Na fada, wadannan mutanen ba za su taba tuba ba sun tuba ne kawai saboda yunwa shikenan.
Yan Bindiga Sun Tsere bayan Sojoji Sun Kakkabe Dajin Kaduna
A wani labari na daban, mun ji cewa yan bindiga sun fara tserewa daga mabuyarsu a garuruwan Kagarko, Iche, Taka-Lafiya Gidan Makeri da Janjala a jihar Kaduna bayan sama da sojoji 100 sun mamaye jejin a karamar hukumar Kagarko.
A yan watanni da suka gabata, garuruwan karkara da dama a masarautar Kagarko sun sha fama da hare-haren yan bindiga wadanda ke sace mazauna da manoma.
Asali: Legit.ng