FG Za Ta Raba Wa Mutane Sama Da Miliyan 1 Tallafin N50k Kowanensu, Tinubu

FG Za Ta Raba Wa Mutane Sama Da Miliyan 1 Tallafin N50k Kowanensu, Tinubu

  • Kyautata rayuwar 'yan Najeriya na ɗaya daga cikin maunufofin da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bai wa fifiko
  • A jawabin kai tsaye da ya yi wa yan Najeriya ranar Litinin, shugaba Tinubu ya sanar da shirinsa na faɗaɗa ayyukan masana'antu don samar da ayyukan yi
  • Shugaban ƙasar ya kuma bayyana cewa FG zata tallafa wa kananan 'yan kasuwa 1,300 da N50k a kowace ƙaramar hukuma

FCT Abuja - Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ta lashi takobin tallafawa kanana da matsakaitan sana'o'i a faɗin Najeriya.

Shugaba Tinubu ne ya bayyana haka a jawabin kai tsaye da ya yi wa 'yan Najeriya ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, 2023.

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
FG Zata Raba Wa Mutane Sama da Miliyan 1 Tallafin N50k Kowanensu, Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa zata raba tallafin N50k ga kowane ɗaya daga cikin masu kanana da matsakaitan sana'o'i 1,300 a kowace ƙaramar hukuma.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: NSA Na Shugaba Tinubu Ya Sa Labule Da Gwamnoni 5 a Abuja, Sahihan Bayanai Sun Fito

Shugaban ƙasar ya sanar da cewa gwamnatinsa ta ware biliyan N50bn domin tallafawa kananan yan kasuwa a faɗin ƙananan hukumomin Najeriya 774.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Gwamnatin Tinubu zata farfaɗo da ayyukan masana'antu

Bugu da kari, shugaban ya kara da cewa gwamnatinsa za ta kashe karin Naira biliyan 75 don fadada masana'antu da nufin samar da ayyukan yi ga 'yan Najeriya, inji rahoton Vanguard.

Tinubu ya ce za a kashe kudaden ne daga watan Yulin 2023 zuwa Maris 2024 a matsayin wata hanya ta farfaɗo da kamfanoni aƙalla 75 wanda hakan zai bunƙasa tattalin arziki.

Ya ƙara da cewa tuni gwamnati ta ware kuɗi naira biliyan 125 domin tallafa wa kananan yan kasuwa da kuma ɓangaren masana'antu saboda sunga taka rawar gani wajen bunƙasa arziƙin Najeriya.

Jaridar The Cable ta tattaro shugaba Tinubu na cewa:

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaba Tinubu Ya Sanar da Sabuwar Garaɓasa Ga Ɗaliban Najeriya

"Don karfafa bangaren masana'antu, da kara inganta su domin fadadawa da samar da ayyukan yi masu kyau, za mu kashe Naira biliyan 75 tsakanin watan Yuli 2023 da Maris 2024."

Jerin Sunayen Ministoci 14 da Majalisar Dattawa Ta Tantance Kawo Yanzu

A wani labarin kuma A ranar farko, majalisar dattawa ta samu damar tantance mutum 14 daga cikin sunayen mutum 28 da Bola Tinubu ya naɗa a matsayin ministoci.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku jerin sunayen ministocin da suka tsallake matakin tantancewa a majalisar dattawa da jihohinsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel