Bidiyon Karamin Yaro Yan Dinki Cikin Kwarewa Ya Girgiza Intanet

Bidiyon Karamin Yaro Yan Dinki Cikin Kwarewa Ya Girgiza Intanet

  • Bidiyon wani karamin yaro yana dinki a shagon mahaifiyarsa ya burge mutane da dama a soshiyal midiya
  • A bidiyon wanda ya yadu a TikTok, an gano yaron yana dinka wani kaya inda ya mayar da hankali sukutum a kai
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun jinjinawa karamin yaron inda wasu suka shawarce shi da ya ci gaba da sa azama

Wani karamin yaro ya burge masu amfani da soshiyal midiya saboda kwarewarsa a dinki bayan shafin @stec_clothing0 ta wallafa bidiyonsa a TikTok.

A bidiyon, an gano yaron yana dinki cike da kwarewa a kan wani keken dinki mallakin mahaifiyarsa, wacce ta kasance tela.

Karamin yaro yana dinki
Bidiyon Karamin Yaro Yan Dinki Cikin Kwarewa Ya Girgiza Intanet Hoto: @stecclothing0/TikTok.
Asali: TikTok

Rubutun da yake jikin bidiyon ya bayyana cewa hazikin yaron yana koyon dinki ne a wajen mahaifiyarsa.

Kwarewar karamin yaro a harkar dinki ya burge mutane

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Bar Iyayenta Don Rayuwa Da Saurayi a Daji, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Bidiyon ya yadu sosai a soshiyal midiya inda mutane da dama suka nuna mamaki da sha'awarsu kan kwarewar yaron sannan sun aika masa da sakonni na karfafa gwiwa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai kuma, wasu sun bayyana cewa koda dai yaron na da baiwa, ya zama dole a bi sahun wannan aiki nasa da ilimi.

Martanin jama'a kan bidiyon yaro da ya kware a dinki

@Blessed Tony ta yi martani:

"Wannan abun burgewa ne, don Allah ya kamata iyayensa su san hanyar da ya dosa sannan su kara karatu a kai, yana da baiwa dama."

@wanjirukamau705 ta ce:

"Wannan zai zama mai dinki na kasa da kasa mun tayaka godewa Allah."

@Shirley Kingston ya yi martani:

"Kafin shekara 10, ya kamata ya zama kwararre."

@Wendy Haywood923 ta yi martani:

"Allah ya ci gaba da kwararo albarkarsa a kanka."

Kara karanta wannan

“Ina Son Zama Uwa Ba Aure”: Kyakkyawar Budurwa Ta Ayyana, Ta Ce Ba Za Ta Iya Yiwa Kowani ‘Da Namiji Biyayya Ba

@memory ta yi martani:

"Gaskiya na so kokarin yaron nan."

@Abiti Selemani ta yi martani

"Wow Allah ya yi masa baiwa."

@Karen ta ce:

"Yana da tarin baiwa Allah ya yi masa albarka dannan ya raya shi."

@TR.Mpango ta ce:

"Haka ya kamata mu koyar da su, ba wai shafe tsawon lokaci a aji ba."

Kalli bidiyon a kasa:

Budurwa ta bar gaban iyayenta ta koma zama da saurayi a dokar daji, bidiyon ya yadu

A wani labari na daban, wata matashiyar yarinya mai suna Mercy daga cikin Delta ta haddasa cece0-kuce a TikTok bayan bidiyonta ya bayyana.

An gano yarinyar tana rayuwa a daji tare da saurayinta wanda ya fito daga jihar Akwa Ibom kuma yana aiki ne a wata gonar koko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng