Bidiyon Batanci: An Haramta Lika Hoton Davido Ko Saka Wakarsa a Kasuwar Waya Ta Kano
- Har yanzu al'ummar Musulmi na ci gaba da jin zafin bidiyon da mawaki Davido ya saki wanda suke ganin ya yi batanci ga addinin Musulunci
- Shugaban kasuwar waya ta Farm Centre da ke jihar Kano, Hassan Bawasa ya haram lika hoto ko saka wakokin Davido a shagunan da ke kasuwar
- Kamar yadda ya sanar, duk wanda aka kama da aikata haka za'a dauki mummunan mataki a kansa
Kano - An haramtawa masu shaguna a kasuwar waya ta Farm Centre da ke jihar Kano lika hotuna ko sauraron wakokin shahararren mawakin Najeriya, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido a shagunansu.
Kamar yadda mai sanarwar ya bayyana, shugaban kasuwar, Hassan Abubakar Bawasa shine ya bayar da umurnin, yana mai gargadin cewa duk wanda aka kama ya karya dokar zai dandana kudarsa.
“Aikin Nan Akwai Hatsari Sosai”: Mai POS Ta Fashe Da Kuka Bayan Ta Karbi Jabun N100K Daga Kwastoma, Bidiyon Ya Yadu
An haramta lika hoto ko saka waka ko bidiyon Davido a kasuwar Farm Centre, Kano
Ya kara da cewar an sanya takunkumin ne sakamakon batancin da Davido ya yi wa addinin Allah, addinin gaskiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ga yadda sanarwar ta zo:
"Dukkan wanda ya san ya lika hoton Davido da ya gaggauta cire shi ya banka masa wuta, sakamakon batancin da ya yi wa addinin gaskiya, addinin Allah, addinin mutanen kasuwar waya na Farm Centre.
"Bayan haka, sanya odiyo ko bidiyo na Davido a teburinka ko a shagonka ya zama haramun a kasuwar waya ta Farm Centre. Idan aka kama ka, za a dauki kwakkwaran mataki na ladabtarwa ta yadda za ka dandana kudarka. Sanarwa daga Hassan Bawasa."
Kalli bidiyon sanarwar wanda shafin codedblog ya wallafa a Instagram
Legit.ng ta tuntubi Mallam Bashir Ibrahim wanda ya kasance dila ne a kasuwar wayan inda ya tabbatar da dokar.
Mallam Ibrahim ya ce:
"Eh tabbas da gaske ne an saka wannan doka daga hukumar kasuwar."
Da aka tambaye shi game da tasirin da wannan doka yi mallam Bashir ya ce lallai ya yi tasiri domin sun daina jin wakar a kasuwar.
Ya ce:
"Ai yayi tasirima tunda mun dai najii."
Kungiyar MURIC ta nemi DSS ta gayyaci mawaki Davido kan bidiyon batanci
A baya Legit.ng ta rahoto cewa Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi kira ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da ta gayyaci Davido da Logos Olori kan bidiyonsu wanda ya nuna rashin da'a ga addinin Islama.
Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya yi kiran a cikin wata sanarwa da ya saki a ranar Litinin, 24 ga watan Yuli, a Abuja, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Asali: Legit.ng