Jihohin Bayelsa, Akwa Ibom Na Kan Gaba a Jerin Jihohin Da Ke Fama Da Talauci a Yankin Kudu Maso Kudu
- Wani sabon rahoto ya nuna tsabagen talaucin da ake fama da shi a jihohin yankin Kudu maso Kudu duk da arziƙin man fetur da su ke da shi
- Jihohin Rivers, Cross Rivers, da Akwa Ibom suna da yawan mutane waɗanda su ke rayuwa cikin ƙangin talauci
- A cewar rahoton, jihar Bayelsa ita ce inda talaucin ya fi yin ƙamari, inda ake samun mutum biyu cikin mutum uku na rayuwa cikin talauci
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
A wani sabon rahoto na wani kamfanin tattara bayanai, SatiSense, rahoton hukumar ƙididdiga ta ƙasa ya nuna talaucin da ake fama da shi a jihohin yankin Kudu maso Kudu na Najeriya.
Rahoton ya bayyana tsabagen talaucin da ya yi wa mutanen yankin na Niger Delta katutu, duk da arziƙin man fetur da yake da shi.
Jihohin yankin Kudu maso Kudu masu fama da matsanancin talauci
Jihohin sun haɗa da Akwa Ibom, Rivers, Cross River, Edo, Delta, da Bayelsa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rahoton ya nuna cewa jihohin Akwa Ibom da Cross River sun fi fama da matsanancin talauci, inda mutum miliyan 5.08 da miliyan 4.4 million ke rayuwa cikin halin babu.
Alƙaluman jihar Akwa Ibom sun nuna cewa kaso 71% na yawan mutanenta na rayuwa cikin talauci.
Haka kuma a jihar Rivers, mutum miliyan 4.4 ke rayuwa cikin talauci wanda hakan ya ɗauki kaso 62.4% na yawan mutanen jihar miliyan 7.47.
Jihar Cross River na fama da matsanancin talauci, inda kaso 75.6% na mutanen jihar ke rayuwa cikin ƙuncin talauci.
Jihohin Edo da Delta, waɗanda basu da yawan mutane sosai, suna fama da tsananin talauci a tsakanin al'ummar jihohin.
Talauci ya fi ƙamari a jihar Bayelsa
Buinessday ta rahoto cewa jihar Edo tana da adadin mutane miliyan 1.4 da su ke rayuwa cikin talauci, wanda hakan ya ƙunshi kaso 35.4% na yawan mutanenta miliyan 3.9, sannan jihar Delta na da mutane miliyan 2.73 masu rayuwa cikin talauci wanda hakan ya nufin kaso 50% na mutanen jihar.
Jihar Bayelsa ce a sama cikin jihohin yankin masu fama da talauci inda kusan mutum miliyan 2.61 ke rayuwa cikin talauci wato kaso 88% na al'ummar jihar mutum miliyan 2.9 na rayuwa cikin talauci.
Jihohin Da Suka Fi Shiga Matsi Kan Cire Tallafin Man Fetur
A wani labarin kuma, bayan cire tallafin man fetur da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi, an shiga cikin halin matsin tattalin arziƙi a ƙasa.
Jihohin yankin Arewacin Najeriya sun fi ji a jikinsu a sakamakon cire tallafin man fetue ɗin, domin farashin man fetur ya fi tsada a yankin idan aka kwatanta da sauran yankunan ƙasar.
Asali: Legit.ng