Da Dumi-Dumi: Majiya Ta Bayyana Wanda Zai Zama Atoni Janar Na Tarayya

Da Dumi-Dumi: Majiya Ta Bayyana Wanda Zai Zama Atoni Janar Na Tarayya

  • An rahoto cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya yanke shawarar nada Lateef Fagbemi a matsayin atoni janar na tarayya kuma ministan shari'a
  • Fagbemi ya kasance babban lauyan da ke kare Tinubu da APC a kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban kasa
  • Shugaban kasar da jam'iyyarsa sun nada babban lauyan Najeriyan ne jim kadan bayan INEC ta sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023

Rahotanni sun kawo cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya shirya gabatar da jerin sunayen ministocinsa a gaban majalisar dokokin tarayya a yau Alhamis, 27 ga watan Yuli.

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa akwai yiwuwar Lateef Fagbemi zai zama zabin shugaban kasa Tinubu domin ya zama Atoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a, rahoton Vanguard.

Tinubu zai nada lauyan APC a matsayin ministan shari'a
Da Dumi-Dumi: Majiya Ta Bayyana Wanda Zai Zama Atoni Janar Na Tarayya Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Babban lauyan APC zai zama AGF

Kara karanta wannan

El-Rufai Na Iya Zama Ministan Wutar Lantarki Yayin da Jerin Sunayen Ministoci Ya Isa Gaban Majalisar Dattawa

Fagbemi ya kasance lauyan da ke kare jam'iyyar All Progressives Congress (APC) a shari'ar zaben shugaban kasa da ke gudana a kotu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Babban lauyan Najeriyan ya kasance kwararren lauya wanda ya gudanar da shari'o'i da dama kan lamuran zabe.

Jim kadan bayan zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, mai ba APC shawara kan harkokin shari'a, Ahmad Usman El-Marzuq ya ce:

"Prince Lateef Fagbemi SAN babban lauya da ya jagoranci manyan shari'o'in zabe daban-daban shine zai jagoranci tawagar lauyoyi da ya kunshi manyan lauyoyin Najeriya 12 da mai ba jam'iyyar shawara kan doka, Usman El-Marzuq, Esq."

Yadda Fagbemi ya zama babban lauyan APC da Tinubu

Shugaban hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC), Mahmood Yakubu ya ayyana Shugaban kasa Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

An Gama Komai, El-Rufai, Wike, Oyetola da Edun Za Su Zama Ministocin Bola Tinubu

Sai dai wasu jam'iyyun siyasa da suka hada da People's Democratic Party da Labour Party sun yi watsi da nasarar Tinubu.

Sun bayyana cewa anyi magudi a zaben sannan suna neman kotun zaben ta ayyana yan takararsu na PDP, Atiku Abubakar da Peter Obi na Labour Party a matsayin wadanda suka lashe zaben.

El-Rufai na iya zama ministan wutar lantarki

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata majiya ta ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya samu shiga jerin ministocin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Majiyar ta ce ana iya mikawa tsohon ministan Abujan ragamar kula da ma'aikatar wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng