Yar Najeriya Da Ta Haifi Tagwaye Ta Sake Haihuwar Yan Uku, Bidiyon Ya Dauka Hankali

Yar Najeriya Da Ta Haifi Tagwaye Ta Sake Haihuwar Yan Uku, Bidiyon Ya Dauka Hankali

  • Wata mata yar Najeriya ta nuna farin cikinta a soshiyal midiya bayan ta haifi kyawawan yara uku masu cike da koshin lafiya
  • A cewar uwar yaran biyar, ta fara haihuwar yan biyu lokacin da ta samu cikinta na farko
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun yi martani ga bidiyon inda wasu da dama suka ji ina ma ace sune

Wata mata yar Najeriya ta ja hanka;i sosai a soshiyal midiya bayan ta haifo yara biyar a haihuwa biyu kacal.

A cewar uwar mai cike alfahari, ta fara haihuwar tagwaye a cikinta na farko.

Ta haifi yara biyar cikin shekaru 2
Yar Najeriya Da Ta Haifi Tagwaye Ta Sake Haihuwar Yan Uku, Bidiyon Ya Dauka Hankali Hoto: @mamatwins100/TikTok.
Asali: TikTok

Jim kadan bayan nan, ta sake haihuwar lafiyayyun yara yan uku sannan ta cika da godiyar Allah.

A cikin wani bidiyo, ta baje kolin yaranta biyar dauke da wani rubutu mai tsuma zukata wanda ya haifar da martani daga jama'a.

Kara karanta wannan

“Na Samu Kudi Ba Na Wasa Ba”: Budurwa Ta Taka Rawa a Wajen Jana’izar Mahaifinta, Ta Baje Makudan Kudin Da Ta Samu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ku ga abun da Allah ya yi mani cikin shekaru biyu. Da farko yan tagwaye, na biyu yan uku. Ina mika dukkan godiyata ga Allah," ta rubuta.

Jama'a sun yi martani

@goldenheart842 ta ce:

"Na tayaki murna. Na tayaki murna. Na tayaki murna. Allah ya yi mun irin wannan Amin."

@ceciliabanda22 ta rubuta:

"Na tayaki murna yar uwa kuma ina rokon Allah ya yi mun irin wanna."

@goldeneso ta ce:

"Na tayaki murna masoyiya kuma na karbi wannan da tarin albarka."

@tracyebune ta ce:

"Mashaa Allah ina tayaki murna da ke da iyalinki."

@uzoechinachinenyeta yi martani:

"Ina tayaki murna yar'uwa, lallai Allah ya albarkace ki, maman yan uku."

@omwana88 ta yi martani:

"Ina tayaki murna. Allah ya kare su har girmansu da sunan Yesu."

@specialsharon2 ta yi martani:

"Na tayaki murna yar'uwa na shafa daga wannan albarka."

Kara karanta wannan

“Ina Son Zama Uwa Ba Aure”: Kyakkyawar Budurwa Ta Ayyana, Ta Ce Ba Za Ta Iya Yiwa Kowani ‘Da Namiji Biyayya Ba

@osasufaith ta yi martani:

"Barka da arziki Na tayaki murna sosai."

Kalli bidiyon a kasa:

Tagwaye Da Suka Auri Yan Tagwaye a Rana Daya Sun Haifi Yan Bibbiyu

A wani labarin kuma, mun ji cewa wani hoto da ke yawo a soshiyal midiya ya nuno wasu jarirai hudu da wasu tagwayen mata biyu suka haifa.

Tagwayen matan ne suka haifi yaran hudu a matsayin yan bibbiyu yan awanni a tsakani, kuma sun yi aure ne a rana guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng