“Na Yi Kudi a Wajen Jana’izar Mahaifina”: Budurwa Ta Taka Rawa a Bidiyo, Ta Baje Kudin Da Ta Samu

“Na Yi Kudi a Wajen Jana’izar Mahaifina”: Budurwa Ta Taka Rawa a Bidiyo, Ta Baje Kudin Da Ta Samu

  • Wata kyakkyawar mata yar Najeriya ta gaza boye farin cikinta yayin da ta kirga kudaden da ta samu a wajen jana'izar mahaifinta
  • A wani bidiyo da aka gano a TikTok, an gano ta tana taka rawa cikin farin ciki yayin da ta baje kolin kudin da ta samu
  • Masu amfani da soshiyal midiya sun bayyana ra'ayoyinsu kan bidiyon inda wasu suka kalli abun a matsayin mai ban dariya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wata mata yar Najeriya ta saki wani bidiyo mai jan hankali daga bikin jana’izar mahaifinta da aka gudanar kwanan nan.

A wani bidiyo da ya yadu, matar mai suna @vickyblack201 a TikTok ta taka rawa cikin farin ciki yayin da ta baje kolin damin kudin da ta samu.

Yar Najeriya ta taka rawa a wajen jana'izar mahaifinta
“Na Yi Kudi a Wajen Jana’izar Mahaifina”: Budurwa Ta Taka Rawa a Bidiyo, Ta Baje Kudin Da Ta Samu Hoto: @vickyblack201/TikTok.
Asali: TikTok

Yayin da take wallafa bidiyon, ta nuna farin cikinta kan kudin da ta samu a wajen bikin binne mahaifin nata.

Kara karanta wannan

Yar Najeriya Da Ta Haifi Tagwaye Ta Sake Haihuwar Yan Uku, Bidiyon Ya Dauka Hankali

Kalamanta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Yanayina saboda na samu kudi a wajen wannan bikin binne baban nawa."

Jama'a sun yi martani

Da suke martani kan bidiyon, mutane da dama sun garzaya sashin sharhi domin bayyana ra'ayoyinsu. Sai dai kuma, abun ya baiwa wasu mamaki.

@prettyfavour24 ta ce:

"Baaba kudin ne ya dame ki."

@neena_laly ta vayyana cewa:

"Ni kenan a shekarar bara amma yanzu kudin ya kare. Tsadar rayuwar Lagas ba na mai rauni bane."

@marianscocktailsta ce:

"Bayan bikin mutuwar mahaifina. Washegari na yi amfani da kudin na siya waya."

@johnqwindalineijay ya ce:

"Mutumin da ya mutu, na shi ne ma ya fi na kowa muni. Wai ace diyar wani ce. Tana jin dadi saboda naira 20 20. Bayan kin san cewa ba za ki kara ganin mahaifinki ba."

@beadsbychristy ta rubuta:

"Ni da mahaifina ya mutu bayan na girma na samu kudi sosau a wajen bikin mutuwarsa. Ina kewansa wasu lokutan dai amma wanda ya tafi ya tafi."

Kara karanta wannan

“Ina Son Zama Uwa Ba Aure”: Kyakkyawar Budurwa Ta Ayyana, Ta Ce Ba Za Ta Iya Yiwa Kowani ‘Da Namiji Biyayya Ba

Kalli bidiyon a kasa:

Ba zan iya bin namiji sahu da kafa ba, budurwa ta ce tana son zama uwa ba aure

A wani labari na daban, wata budurwa yar Najeriya, @thearabicgirl_skincare0, ta bayyana cewa ta so ta zama uwa ba tare da aure ba amma bata san yaya za ta sanar da mahaifiyarta ba.

A cewarta, ba za ta iya daukar umurni daga kowani 'da namiji ba kuma saboda haka bata tunanin yin aure.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng