Abbas Ya Kafa Kwamiti a Majalisa, Za Su Gana Da Tinubu Kan Shirin Shiga Yajin Aikin Likitoci
- Majalisar wakilai na yin duk wacca za su iya don dakile shirin shiga yajin aikin da kungiyar likitocin Najeriya ke yi
- Daga cikin kokarin da yake yi na hana yunkurin, kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, na shirin ganawa da shugaban kasa, Asiwaju Bola Tinubu
- A cewar Abbas wannan ganawar na da matukar muhimmanci domin zai magance da samo maslaha ga yajin aikin likitocin
FCT, Abuja - Kakakin majalisar wakilai, Honourable Tajudeen Abbas, na shirin ganawa da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Jaridar Punch ta rahoto cewa ganawar da za a yi tsakanin Abbas da shugaban kasar na daga cikin kokarin da ake yi na dakile shirin da kungiyar likitocin Najeriya (NARD) ke yi na shiga yajin aiki.
Batutuwan da za su tattauna
Abbas ya kuma bayyana cewa zai gana da Tinubu ne domin sanar da shi batutuwan da kungiyar NARD ta gabatar tare da kira ga shugaban kasa kan yadda zai warware su.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hakan na zuwa ne yan awanni bayan kakakin majalisar ya bukaci fusatattun likitocin da su janye yajin aikin da suke shirin shiga da kuma ba majalisar damar yin tunani a kan al’amuran da ke gabansu, rahoton Nigerian Tribune.
A yayin ganawa da shugabancin NARD na kasa a ofishinsa da ke Abuja, a ranar Litinin, Hon. Abbas ya kuma sanar da kafa wani kwamitin wucin gadi karkashin jagorancin shugaban majalisa, Farfesa Julius Ihonvbere.
Kwamiin zai gana da dukkan masu ruwa da tsaki domin magance lamuran, jaridar Leadership ta rahoto.
Fasto ya bukaci APC da ta zabi Al-makura a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa maimakon Ganduje
A wani labari na daban, Primate Elijah Ayodele, shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual ya ce mutumin da ya fi dacewa da shugabancin jam'iyyar All Progressive Congress (APC) shine tsohon gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura.
Malamin addinin wanda ya yi suna wajen yin hasashe ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinsa, Osho Oluwatosin.
Asali: Legit.ng