Ku Tuka Motocin Innoson, Ku Yi Amfani da Glo: Omokri Ya Lissafo Abubuwa 20 Da Za Su Sa Naira Ta Yi Daraja

Ku Tuka Motocin Innoson, Ku Yi Amfani da Glo: Omokri Ya Lissafo Abubuwa 20 Da Za Su Sa Naira Ta Yi Daraja

  • An bukaci yan Najeriya da su dunga siyan kayayyakin Najeriya domin taimakawa wajen inganta asusun ajiyar kasar a waje
  • Reno Omokri ya ambaci abubuwan da ya zama dole yan Najeriya su yi domin taimakawa wajen daga darajar naira a kan sauran kudade
  • Ya ce Naira za ta kara daraja sannan kayayyaki da ayyukan Najeriya su ma za su kara inganci idan yan kasar suka koma siyansu

Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Reno Omokri, ya lissafa abubuwa 20 da ya kamata yan Najeriya su yi don daga darajar naira a kan sauran kudaden duniya.

Omokri ya ce yan Najeriya ne kadai za su iya ceto Najeriya ta hanyar siyan kayayyakin da aka yi a gida.

Reno Omokri ya fadi hanyar farfado da darajar Naira
Ku Tuka Motocin Innoson, Ku Yi Amfani da Glo: Omokri Ya Lissafo Abubuwa 20 Da Za Su Sa Naira Ta Yi Daraja Hoto: @renoomokri
Asali: UGC

Ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 21 ga watan Yuli, ta shafinsa na Twitter @renoomokri, yana mai cewa ci gaba da siyan kayan da aka yi a Najeriya zai taimaka wajen inganta kayan.

Kara karanta wannan

Hukumar FIRS Ta Tara Tiriliyan 5.5 a Watanni 6, Harajin Da Ba a Taba Samu a Tarihi Ba

Omokri ya ce ya kamata yan Najeriya su fara amfani da layukan Glo maimakon MTN, Airtel ko Etisalat, su siya motar Innoson maimakon Marsandi, Range Rover ko Honda.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta:

"1. Maimakon MTN, Airtel ko Etisalat, ku yi amfani da Glo
2. Maimakon Mercedes, Range Rover, ko Honda, ku siya Innoson
3. Ku shiga jirgin Air Peace bisa Air France, KLM, ko Lufthansa
4. Ku yi amfani da First Bank, UBA, GTBank, da Zenith bisa Stanbic
5. Ku kalli AriseTV, Channels da NTA maimakon DSTV
6. Ku siya simintin Dangote da Ibeto cement, sannan ku guji jkayan China
7. Ku siya da siyanEnyimba FC, Kano Pillars, da 3SC kan Manchester United, Barcelona, PSG, da Napoli
8. Ku siya wakokin Najeriya maimakon sanya na mawakan waje

Kara karanta wannan

‘Yan NWC ba su Goyon Bayan Zaman Ganduje Sabon Shugaban Jam’iyyar APC

9. Ku siya DAKOVA, Mai Atafo, Mudi Africa, da JADZ Couture (masu yin babanriga da agbada. ku nuna mata kauna +234 704 477 9973) kan Armani, Gucci, Balenciaja, da Louis Vuitton
10. Ku sa burkutu kan champagne, Hennessy, Scotch Whiskey, da Irish Cream
11. Ku yi siyayya daga mata yan kasuwa maimakon zuwa Shoprite
12. Ku siya da dafa shinkafa yar gida sannan ku hakura da cin shinkafa yar Thailand
13.Ku duba yiwuwar cin biredin rogo bisa ga wanda ake yi da filawa yar waje.
14. Ku siya Zinox PCs, laftof da waya
15. Maimakon Birdseye custard, Quaker oats, da Kellogg' ku sha akamu, kunu da koko
16. Ku hakura KFC, sannan ku koma ga e Mr Bigg's, Tantalizers, da abincin titi
17. Ku daina amfani da Holland Wax, da atamfpfin waje. Ku yi amfani da shaddodin Kaduna, saki, da sauran zanuwan gida.
18. Ku rage kallon fina-finan Hollywood da Bollywood sannan ku koma ga fina-finan Nollywood da Kannywood

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya, Gwamnoni Za Su Raba Kudin Da Ya Fi Kowane Yawa a Tarihin FAAC

19. A je hutu da yawon amarci a Obudu Cattle Ranch, Yankari Games Reserve, Ikogosi Warm Springs, sannan ku halarci bikin kamun kifi na Argungu
20. Ku yi watsi da daskararrun kifi yan waje, nama da dauransu sannan ku rungumi kayayyakin cikin gida.

PDP ta hango abun da zai faru idan kotu ta tsige Tinubu

A wani labarin, jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) mai adawa ta bayyana abun da zai faru idan kotun zaben shugaban kasa ta soke nasarar zaben jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ranar 25 ga watan Fabrairu.

PDP ta bayyana cewa yan Najeriya za su fita tituna don murna idan kotu ta soke nasarar shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng