“Ka Dawo Da Shi”: Wani Mutum Ya Ce Sai Ya Karbi N80 Da Mai Wanki Ya Gani a Aljihunsa
- Wani mai wanki da guga ya tsinci kudi a aljihun daya daga cikin kwastamominsa sai ya yanke shawarar sanar da shi
- Nan take mutumin ya turawa mai wankin lambar asusunsa na banki, inda ya bukaci ya gaggauta tura masa kudin
- Hirarsu na Whatsapp wanda ke nuna yadda aka fara tattaunawa tsakanin mai wankin da kwastaman ya baiwa mutane dariya
Wani mutumin ya bukaci mai yi masa wanki da guga da ya gaggauta dawo masa da kudin da ya tsinta a aljihunsa yayin da yake wanke masa kaya.
Mai wanki da gugan ya tsinci N80 a aljihun kwataman nasa sannan ya sanar da shi ta Whatsapp.
Idan ma mai wanki da gugan na tunanin kwastaman zai ce masa ya rike kudin ne, toh ya yi kuskure saboda bai ce ba.
“Karin ‘Da 1 Kacal Na Nema”: Magidanci Ya Koka Yayin da Matarsa Ta Haifo Tagwaye, Ta Mika Masa Su a Bidiyo
Maimakon haka, kwatsaman ya dage kan cewa ya tura masa kudin zuwa asusun bankinsa, wanda ya turawa mai wanki da gugan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Nan take da mai wankin ya sanar da shi cewa ya tsinci N80 a aljihunsa, sai mutumin ya tura masa da lambar asusunsa na banki sannan ya ce ya tura masa kudin a ciki.
Hirar ban dariya da ya gudana tsakanin mutumin da mai wankinsa ya baiwa mutane da dama dariya bayan Timilehin Daniel Ade ya wallafa shi a Twitter.
Kalli wallafarsa a kasa:
Jama'a sun yi martani
@TundeOlowo2 ya ce:
"Ko wani taro da kwabo na da muhimmanci dan uwana lol."
@meggiebangz ta yi martani:
"Kalli kanka."
Wani mutum ya roki barawon da ya sace masa waya, ya bukaci ya turo masa lambar 'Sugar Mummy'
A wani labarin kuma, wani matashi da ya rasa wayarsa sakamakon sacewa da wani ya yi a wajen wata zanga-zanga ya roki barawon wayar da ya tura masa da wata lamba mai matukar muhimmaci a gare shi zuwa shafinsa na Facebook.
Matashin mai suna Silvanus wanda ya kasance dan kasar Kenya ya nemi barawon wayar ya tura masa lambar budurwarsa wacce yake yi wa lakabi da 'mercy my suga' domin a cewarsa ita ce ke taimaka masa da bukatun kudi ciki harda biya masa kudin hayar gidan da yake ciki a yanzu.
Asali: Legit.ng