“Menene Wannan?” Budurwa Ta Dafa Taliyarta Da Lemun Mirinda da Sukari a Bidiyo
- Masu amfani da soshiyal midiya sun caccaki wata yar Najeriya kan wani bidiyonta tana dafa taliya da lemun kwalba
- Bayan ta yi amfani da Mirinda, budurwar ta kuma kara sukari a cikin abinci, cewa zai kara masa dandano
- Wasu mutane sun caccaketa kan yadda take neman suna ta hanyar girka kwamacala, wasu kuma suna ganin bata da lafiyar kwakwalwa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata matashiya yar Najeriya, Cyndy ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta baje kolin taliyar da ta dafa inda ta yi amfani da lemun Mirinda da Sukari.
Cyndy, mai nishadantarwa a TikTok ta baje kolin yadda ta girka taliya a cikin yar tukunyar suya da risho mai amfani da gas.
Ta fara da juye lemun kwalba a cikin tukunyar suya sannan ta bi sahunsa da taliya kafin ta zuba atarugu, sinadarin dandano da kuma albasa.
Bayan ta gama, sai ta zuba abincin a cikin kwano sannan ta kara sukari a ciki, cewa zai kara masa dadi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Bidiyon ya kare a daidai lokacin da take shirin kai abincin mai ban mamaki bakinta. Jama'a sun caccake ta kan dafa abinci da lemun kwalba.
Kalli bidiyon a kasa:
Mutane sun caccaki budurwar
@_S I M I L A ya ce:
"Don Allah yaushe za ki yi bidiyon kashi na 2. Don Allah ki sanya lokacin da kika ziyarci bandaki a ciki."
Mimo baby ta ce:
"Nima bana son abubuwa da yawa a ciki. Kuma na kan so zuba kananzir yana sa shi dadi."
TOM ya ce:
"Duk irin abubuwa haka kamar wasa suke farawa...daga nan kafin ki sani ya zame maki jiki."
E G C money ya ce:
"Ba ku ga fuskarta ba ta kwale da yawa ta sha colos kadan."
user7355988781883 ya ce:
"Don Allah saura abun goge hakora da man injin."
stars_delight ta ce:
"Biyu da safe biyu da rana sannan biyu da daddare, Allah ya baki lafiya yar'uwa."
Bidiyon wata mata tana tuka amala da na'ura ya dauka hankali
A wani labarin kuma, wata mata ta tashi kan yan mata da dama a soshiyal midiya bayan bayyanan bidiyonta tana tuka amala da na'ura maimakon muciya.
Da dama sun ce yanzu sun shirya aure domin ga dukkan alamu ba za su sha wahala ba a gidajensu.
Asali: Legit.ng