“Sai Ka Yi Aiki”: Matashi Da Ya Roki Matarsa Ta Kara Haihuwar ‘Da 1 Ya Samu Tagwaye, Ya Koka a Bidiyo

“Sai Ka Yi Aiki”: Matashi Da Ya Roki Matarsa Ta Kara Haihuwar ‘Da 1 Ya Samu Tagwaye, Ya Koka a Bidiyo

  • Wani uba da ya roki matarsa ta kara haifa masa 'da daya ya samu kari a kan abun da ya nema
  • A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano mutumin dauke da yan tagwayensa sannan ya koka cewa aikin ba mai sauki bane a gare shi
  • Jama'a da suka ci karo da bidiyon sun sha mamaki yayin da suka shawarci mutane da su yi hankali da abun da suke so

Wani magidanci ya samu fiye da abun da ya nema bayan ya bukaci matarsa da ta haifa masa karin 'da daya.

Mutumin mai suna @mr_and_mrs_levy a TikTok ya saki hotonsa yana fama da daukar yan tagwayen nasa.

Ya nemi matarsa ta karo da 1 amma sai aka samu yan 2
“Sai Ka Yi Aiki”: Matashi Da Ya Roki Matarsa Ta Kara Haihuwar ‘Da 1 Ya Samu Tagwaye, Ya Koka a Bidiyo Hoto: @mr_and_mrs_levy/TikTok.
Asali: TikTok

A bidiyon, ya yi iya bakin kokarinsa don lallashin yaran yayin da su dukka biyun suka dungi kuka a hannunsa.

Kara karanta wannan

“Na Kusa Zaucewa”: Matashi Ya Sharbi Kuka Bayan Ya Farka Bacci Ya Ga Dakinsa Cike Da Ruwa, Bidiyo Ya Bayyana

A cewar Levi ya roki matarsa a kan ta haifa masa 'da daya kacal amma sai ta haifo masa tagwaye.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta a jikin idiyon:

"Lokacin da na roki matata da ta haifo mun karin 'da daya sai ta haifo mani 2."

Jama'a sun yi martani

Bidiyon ya haddasa cece-kuce inda iyaye da dama suka magantu kan kalubalen da ke tattare da kula da tagwaye.

Wasu kuma sun zolayi matashin yayin da matarsa ta mika masa yaran domin ya kula da su.

@NeishaB ta yi martani:

"Kakata ta haifi yan biyu sau 3 kuma mahaifiyata na daya daga cikinsu. Tuni na fara damuwa."

@sabrinamelinda95 ya ce:

"Sai da tabbata ta baka 2 don kada ka sake neman kari!"

@sassychrissy ta ce:

"Wayyo Allah rayuwata a watanni biyu masu zuwa."

@Luckybabymom ta yi martani:

Kara karanta wannan

“Namiji Baya Kadan”: Wata Mata Yar Najeriya Ta Baje Kolin Saurayinta Mai Karancin Shekaru

"Albarka biyu kada ka damu."

@mariam k 615 ta yi martani:

"Ka ji dadinka ka samu abun da kake so sau biyu."

@becky ta ce:

"Tafiyar za ta kasance mai wahala faaa."

Matashi ya fashe da kuka bayan ya wayi gari ya ga kansa tsamo-tsamo a cikin ruwa

A wani labari na daban, wani matashi dan Najeriya ya yi kuka da hawaye yayin da ya farka daga bacci sannan ya ga dakinsa ya cika da ruwa sakamakon barin famfon bandakinsa da ya yi a bude.

A wani bidiyon TikTok, mutumin ya nunawa jama'a gidan nasa da ya cika da ruwa sannan ya baje kolin famfon da ke zuba a bandaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng