Dan Najeriya Ya Koka Bayan Ya Wayi Gari Ya Ga Dakinsa Cike Da Ruwa

Dan Najeriya Ya Koka Bayan Ya Wayi Gari Ya Ga Dakinsa Cike Da Ruwa

  • Wani dan Najeriya ya shiga wani hali bayan ya kwanta bacci da famfon bandakinsa a bude
  • Gaba daya dakin ya cika da ruwa kuma hakan ya sa shi sharbar kuka wiwi kafin ya fara aikin kwashe ruwan
  • Wani bidiyo da ya saki ya nuno dakin da ya cika da ruwa kuma ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani matashi dan Najeriya ya yi kuka da hawaye yayin da ya farka daga bacci sannan ya ga dakinsa ya cika da ruwa sakamakon barin famfon bandakinsa da ya yi a bude.

A wani bidiyon TikTok, mutumin ya nunawa jama'a gidan nasa da ya cika da ruwa sannan ya baje kolin famfon da ke zuba a bandaki.

Gida ya cika da ruwa sakamakon barin famfo a bude
Dan Najeriya Ya Koka Bayan Ya Wayi Gari Ya Ga Dakinsa Cike Da Ruwa Hoto: @_munach
Asali: TikTok

A cewarsa, bacci ya dauke shi sannan ya manta bai rufe famfon bandakinsa ba. Mutumin ya ce ya shafe tsawon awanni biyu yana kuka kafin ya fara aikin goge-goge.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Ya Makance Yayin da Yake Kokarin Shiga Kundin Bajinta Na Guinness Ta Hanyar Kuka Na Kwanaki 100

An gano shi yana goge dakin tare da kwashe ruwan a cikin wani bokiti yayin da ya dunga kokarin kimtsa wajen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Jama'a sun tausaya masa, inda wasu da dama suka bayyana cewa irin haka ya taba faruwa da su.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Amokeh ta ce:

"Wannan abun ya faru da ni jiya amma koda dai koda na bar shi na mako guda, ruwa ba zai taba shiga dakina ba."

Dunni Of Lay_Lay ta ce:

"Ya taba faruwa da ni sau daya amma ranar an ji ta dadi ba na zauna na kusan awanni 2 ina kallon firinjina yana yawo a cikin ruwa."

Tresy ta ce:

"Baaba irin wannan abun ya kan faru da ni a makaranta shiyasa idan zan tafi aji ina kara dubawa don tabbatar da famfuna na rufe."

Kara karanta wannan

Tallafin Fetur: Da Ya Sha Suka, Tinubu Ya Janye Tsarin da Ya Yi Niyyar Fito da Shi

ZÍÈ ta ce:

"Baaba ba zan taba mantawa da ranar da abun nan ya faru da ni ba, na kuwa zaucewa."

Highdee___ ta ce:

"Wannan abun akwai ciwo! ya kan faru da ni da nake 200level. Ba mu kan samu ruwa don haka sai na bude famfona da nufin Allah yasa na samu ruwa baaba gadona."

Dan Najeriya ya makance a kokarinsa na son shiga kundin bajinta na Guiness

A wani labari na daban, mun ji cewa Tembu Ebere, wani matashi dan Najeriya, wanda ya yi kokarin shiga gasar kuka, ya tabbatar da cewar ya makance na wucin gadi a yayin da yake kokarin shiga kundin bajintar na duniya.

Mutumin, wanda ke da alaka da kasar Kamaru, ya shahara a kwanakin baya bayan ya fara gasar kuka na tsawon awanni 100 domin shiga kundin bajinta na Guiness na kuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng