Gasar Kuka: Dan Najeriya Ya Makance a Kokarinsa Na Shiga Kundin Bajinta Na Guinness

Gasar Kuka: Dan Najeriya Ya Makance a Kokarinsa Na Shiga Kundin Bajinta Na Guinness

  • Wani dan Najeriya ya magance na wucin gadi yayin da yake kokarin shiga kundin bajinta na Guinness na wanda ya fi kowa dadewa yana kuka
  • Matashin ya magantu kan yadda ya sauya dabara bayan fuskarsa ta kumbura sannan idanunsa suka yi rudu-rudu
  • Halin da ya tsinci kansa a gasar kukan ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da mutane suka soke shi a kan kokarin kafa irin wannan tarihi

Tembu Ebere, wani matashi dan Najeriya, wanda ya yi kokarin shiga gasar kuka, ya tabbatar da cewar ya makance na wucin gadi a yayin da yake kokarin shiga kundin bajintar na duniya.

Mutumin, wanda ke da alaka da kasar Kamaru, ya shahara a kwanakin baya bayan ya fara gasar kuka na tsawon awanni 100 domin shiga kundin bajinta na Guiness na kuka.

Kara karanta wannan

“Na Kadu”: Matashi Dan Shekaru 31 Ya Gano Ainahin Shekarun Amaryarsa Mako 2 Kafin Bikinsu

Tembu ya ce ya makance na dan lokaci
Gasar Kuka: Dan Najeriya Ya Makance a Kokarinsa Na Shiga Kundin Bajinta Na Guinness Hoto: @237_towncryer
Asali: TikTok

Da yake zantawa da sashin BBC, Ebere ya ce dai da ya sauya dabara bayan ya fuskanci wasu kalubale da suka danganci lafiyarsa.

A cewars, ya yi fama da ciwon kai, fuskarsa ta kumbura dannan idanunsa suka yi rudu-rudu, kuma ma har ya magance na tsawon mintuna 45.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sai da na sake dabara sannan na rage kukana," inji shi.

Mutane sun yi martani a kan halin da Ebere Tembu ya shiga

@NELLYFNK1 ta ce:

"Wannan shi ya shafa. Kada wanda ya zo ya ce na bayar da gudunmawar kudi don wani shirme."

@OLAMIDE266 ya ce:

"Na zata gayen nan wasa yake yi a lokacin da ya fara wannan shirmen # ooooo. Koda dai ban yarda cewa ya makance ba."

@IamDynamicV ya ce:

"A kokarinsa na kafa tarihi, ya kare da kafa wani tarihin na daban! "Mutum na farko da ya magance yayin da yake kokarin shiga kundin bajinta na duniya."

Kara karanta wannan

“Saura Kadan Na Haukace”: Matashi Da Ya Sunkuya a Kasuwar Lagas Ya Fadi Abubuwan Ban Tsoro Da Ya Gani

Matashi ya fara kuka na awanni 100 don shiga kundin bajinta na Guinness

A baya Legit.ng ta kawo cewa a kokarinsa na son shiga kudnin bajinta na Guinness, wani mutum ya fara kuka inda zai shafe tsawon awanni 100 yana yi.

A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, an gano mutamin yana kururuwa kamar an sanar da shi labarin mutuwar wani dan uwansa ko wanin abu ya same shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng