Mataimakin Ciyaman Ya Mutu Awanni 72 Bayan Rasuwar Ciyaman a Ondo

Mataimakin Ciyaman Ya Mutu Awanni 72 Bayan Rasuwar Ciyaman a Ondo

  • Mutane sun shiga jimami yayin da mataimakin shugaban ƙaramar hukuma ya mutu kwana 3 bayan mutuwar ciyaman ɗinsa a Ondo
  • Tsohon kwamishinan wasanni, Saka Yusuf Ogunleye, ya ce karamar hukumar Akure ta arewa ta rasa mutanen biyu cikin mako ɗaya
  • Muƙaddashin gwamnan Ondo ya je har gida ta'aziyar rasuwar ciyaman ɗin Akure ta arewa a makon da ya gabata

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ondo - Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Akure ta arewa a jihar Ondo, Mista Anthony Adebusole, ya riga mu gidan gaskiya ranar 16 ga watan Yuli, 2023.

Jaridar The Nation ta tattaro cewa Mista Adebusole ya mutu ranar Lahadi, awanni 72 bayan mai gidansa, Bankole Ogbesetore, ya kwanta dama.

Mataimakin shugaban karamar hukuma Ya Mutu Kwana 3 Bayan mutuwar ciyaman.
Mataimakin Ciyaman Ya Mutu Awanni 72 Bayan Rasuwar Ciyaman a Ondo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa shugaban ƙaramar hukumar Akure ta arewa, Mista Ogbesetore ya mutu ne bayan jinyar wani ciwo da ba'a bayyana ba har kawo yanzu.

Kara karanta wannan

APC Ta Tabbatar da Cewa Shugaba da Sakataren Jam'iyya Sun Yi Murabus, Ta Maye Gurbinsu

A makon da ya gabata, muƙaddashin gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya kai ziyarar ta'aziyya gidan marigayi Ciyaman, Mista Ogbesetore.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan kwana 3 mataimakinsa ya rasu

Tsohon kwamishinan wasanni da ci gaban matasan Ondo, Saka Yusuf Ogunleye, shi ne ya tabbatar da rasuwar mataimakin ciyaman ɗin, Adebusole.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Ogunleye na cewa:

"Cikin takaici da ƙunci ina mai ƙara sanar da rasuwar mataimakin shugaban ƙaramar hukumar mu, Honorabul Anthony Adebusola. Ya kwanta dama jiya (Lahadi 16 ga watan Yuli) bayan fama da gajeruwar rashin lafiya."
"Abun ba daɗi yadda muka rasa zababben shugaban karamar hukumarmu da mataimakinsa mai tsantsar biyayya da sanin ya kamata a cikin mako ɗaya."
"Kamar wani wasan kwaikwayo mara kyau, labari mai ciwo da raɗadi. Ina rokon ku mana Addu'a da kuma iyalan da mutanen biyu suka rasu suka bari.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Bayyana Kan Dalilin Da Ya Sanya Abdullahi Adamu Ya Rasa Mukamin Shugabancin APC

Mista Ogunleye ya bayyana cewa wannan mutuwa guda biyu cikin mako ɗaya ta jefa mutanen yankin Akure ta arewa cikin yanayin jimami da raɗaɗin rashi.

An Gano Gawar 'Dan Sanda Na Musamman' Cikin Yan Bindiga Da Suka Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna A Filato

A wani labarin na daban Rundunar sojin Najeriya da ke karamar hukumar Mangu a jihar Filato ta hallaka ‘yan bindiga uku da suka addabi jama'a.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Burgediya Janar Onyema Nwachukwu shi ya bayyana haka a wata sanarwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262