Tinubu Ya Shawarci Shugabannin Afrika Su Kare Arzikin Kasashensu Daga Amurka Da Kasashen Turai
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike da muhimmin sako ga Amurka, da sauran kasashen Turai
- A taron kungiyar Tarayyar Afrika karo na biyar na tsakiyar shekara, a ranar Lahadi, 16 ga watan Yuli, Shugaba Tinubu, ya caccaki kasashen Turawa cikin kakkausan lafazi
- Ya ce wajibi ne shugabannin Afrika su tsaya tsayin daka wajen magance fasa kwaurin dukiya da kasashen Turawan ke yi musu
Nairobi, Kenya - Shugaba Bola Tinubu ya ce dole ne kasashen Afrika su tashi tsaye wajen magance matsalolin da ke dakile ci gabansu tun shekarun baya.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne ranar Lahadin da ta gabata a wajen taron kungiyar Tarayyar Afrika (AU) na tsakiyar shekara karo na biyar.
Tinubu ya ce ba za a ci gaba da yi wa Afrika mulkin mallaka ba
Kamar yadda jaridar The Punch ta wallafa, shugaban ya ce dole ne kasashen na Afrika su hada kawunansu, wajen dawo da ikon juya dukiyoyinsu karkashin ikonsu domin magance matsalar satar da wasu kasashe ke yi musu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya ce yana so masu kwasar arzikin ƙasashen Afrika su sani cewa, yanzu fa sabbin jini ke mulkar ƙasashen nahiyar.
Ya ce abinda ya faru a baya ya riga da ya faru, amma ba za su bari a sake maimaita hakan a yanzu ba.
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Dele Alake, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bukaci shugabannin Afirka da su jajirce wajen kare dukiyoyinsu daga kasashe 'yan fasa kwauri.
Tinubu kan matsalar tsaro a Afrika
Kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito, Tinubu ya ce kasashen Afrika ba za su samu cigaban da suke mafarki ba muddun ba a samu dawwamammen zaman lafiya ba.
Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Ya Bayyana Yadda Wani Yankin Najeriya Ya Yi Asarar N4trn Cikin Shekara Biyu Saboda Dalili 1 Rak
Tinubu ya ce tashe-tashen hankulan da ake samu a wasu daga cikin kasashen Afrika na daga cikin abinda ke dakile cigabansu.
A dalilin haka ne ya ce ya zama wajibi garesu su tashi tsaye wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin.
Tinubu na dab da ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa 200k
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na dab da sanya hannu kan ƙudurin ƙara mafi ƙarancin albashi zuwa naira 200,000.
Tinubu tun kafin hawansa karagar mulki, ya taɓa iƙirarin cewa ma'aikatan gwamnati za su samu ingantacciyar rayuwa a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng