An Tsinci Gawar Budurwa a Dakin Otel Bayan Sun Kashe Dare Da Saurayinta
- Ma'aikatan wani otel da ke jihar Lagas sun gano gawar wata mata da suka yi masauki a cikin otel din
- Budurwar sun isa otel din ne tare da saurayinta inda suka kama daya daga cikin dakunan da ke ciki
- Sai dai bayan saurayin ya fita da zumar zai je ya dawo, an tsinci gawarta kwance babu riga kuma masoyin nata bai dawo ba
Jihar Lagos - Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an tsici gawar wata matashi mai shekaru 28 a wani dakin otel da ke unguwar 102 Yale Okeowo, hanyar cikin gari, Ago Palace Way, jihar Lagas.
Lamarin ya afku ne a ranar Laraba lokacin da wani matashi ya kama daki otel din tare da budurwa. Bayan wasu yan mintoci, sai ya bar budurwar a cikin dakin.
Matashin mai suna Kelvin kamar yadda takardar otel din ya nuna, shine mutum na farko da ake zargi da aikata laifin.
An tsinci gawar budurwa kwance a kasa babu kaya
A cewar majiyoyi, an gano faruwar lamarin ne a safiyar ranar Alhamis lokacin da aka tsinci gawar budurwar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata ma'aikaciyar otel din da ta nemi a sakaya sunanta, ta sanarwa Sunday Vanguard abun da ya faru.
Ta ce:
"Wani matashi ya isa otel din da misalin karfe 11:00 na yamma a ranar Laraba tare da budurwarsa, wacce ba za ta wuce shekaru 28 ba. Ya biya N9,000 ta asusun banki domin kama daki sannan suka shige dakin tare da ita. Jim kadan bayan nan, ya sauko kasa, yana tambayar lokacin da otel din ke rufe kofa domin yana shirin ziyartan wani gidan rawa na dare.
"Ya ba mu tabbacin cewa zai dawo nan ba da jimawa ba domin dai har lokacin budurwarsa na a cikin dakin. Washegari, duk da yawan kokarin shiga dakin da aka yi ta hanyar kwankwasa kofa, babu wanda ya amsa
"Da aka leka ta windon dakin, sai muka farga saboda mun ga kafar mutum a kasa. Nan take muka sanar da manaja, wanda ya tuntubi ofishin yan sandan Ago Palace. Da aka fasa kofa, sai wani mummunan al'amari ya riske mu: gawar mace kwance jikinta ba kaya a kasa."
Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 7, sun kwato makamai
A wani labarin, mun ji cewa rundunar yan sandan jihar Bauchi ta yi nasarar kama wasu da ake zaton masu garkuwa da mutane ne su bakwai sannan ta kwato makamai guda hudu a karamar hukumar Alkaleri da ke jihar.
Kakakin yan sandan jihar, SP Ahmed Wakil, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Asali: Legit.ng