Tarbiyya: An Yanke Bulala 40 Ko Tarar N10,000 Ga Mata Masu Shugar Banza a Yankin Delta

Tarbiyya: An Yanke Bulala 40 Ko Tarar N10,000 Ga Mata Masu Shugar Banza a Yankin Delta

  • Matasan yankin karamar hukumar Warri ta kudu a jihar Delta sun ɗauri damarar yaƙar shigar rashin ɗa'a da yan mata ke yi
  • Ƙungiyar matasan ta yanke hukuncin Bulala 40 ko tarar N10,000 ga duk macen da aka kama ta yi shigar nuna tsiraici
  • Sun ce ba zasu lamurci yanayin shigar da 'yan matan ke yi da sunan wayewa ba, dole su koya nusu tarbiyya

Jihar Delta - Ƙungiyar matasa mai suna 'Ubeji Youth and Employment Development' da ke ƙaramar hukumar Warri ta kudu a jihar Delta sun ɗauki matakin gyara tarbiyya a yankinsu.

Ƙungiyar ta cimma matsaya kuma ta amince da hukuncin bulala 40 ga kowace matashiyar budurwa da aka kama ta yi shigar rashin ɗa'a ta jan hankali a garinsu.

Taswirar jihar Delta.
Tarbiyya: An Yanke Bulala 40 Ko Tarar N10,000 Ga Mata Masu Shugar Banza a Yankin Delta Hoto: punchng
Asali: UGC

Jaridai Daily Trust ta ranar Asabar ta tattaro rahoton cewa ƙungiyar ta kuma bada zaɓin tarar N10,000 ga duk macen da aka kama da saɓa wa dokar shigar banza a yankin.

Kara karanta wannan

Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai Ya Bayyana Yadda Wani Yankin Najeriya Ya Yi Asarar N4trn Cikin Shekara Biyu Saboda Dalili 1 Rak

Sakataren ƙungiyar matasan, Mista Stanley Bomele, shi ne ya bayyana haka yayin da yake hira da manema labarai a jihar Delta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ƙara da cewa matasa sun yanke fara aiki mai taken, "Yaƙi da shigar banza," a tsakanin matasan 'yan mata a yankin, wanda ke neman zama ruwan dare.

Mista Bemele ya ce wannan matakin ya zama wajibi sakamakon yadda shigar mata ke ƙara lalacewa kullum, sun koma sanya kaya na rashin ɗa'a da rashin tarbiyya a yankin.

An haramta wa mata sa matsattsun kaya?

Bugu da ƙari, Sakataren ya sanar da cewa daga ranar, sun ta haramta wa mata sanya ƙananan Siket (Minisikets) da sauran matsattsun kaya da ke fito da surar jikinsu.

Ya yi gargaɗin cewa ba zasu lamurci ganin 'yan mata na sanya irin waɗan nan kayan ba saboda su ne babbar ƙofar da ke haddasa yawaitar lalata da cin zarafin mata.

Kara karanta wannan

Badakalar N1bn: Kotu Ta Bayar Da Sabon Umarni a Shari'ar Tsohon Kwamishinan Ganduje

Ya ce yanzun da yawan matan yankin sun lalace wajen sanya kaya da sunan wayewa, da yawansu suna fitowa tamkar tsirara, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya ce wannan aikin na hukunta duk wacce ta yi shigar banza zai ci gaba daga nan har zuwa lokacin da matan yankin zasu shiga taitayinsu, su riƙa shiga ta kamala.

Karshen Kyau: Budurwa Ta Gigiza Intanet da Bidiyon Santala-Santalan Kawayenta

A wani labarin na daban kuma Wani bidiyo da wata budurwa ta wallafa wanda ya nuna kyawawan ƙawayenta a cikin kayan makaranta ya ja hankali.

Bidiyon ya nuna yadda santala-santalan matan suka sanya fararen hijabai kuma suna yi wa kamarar da ke ɗaukarsu murmushi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262