“Yanzu Na Mallaki Gidan Kaina”: Yar Shekara 19 Ta Baje Kolin Karamin Gidan Da Ta Ginawa Kanta

“Yanzu Na Mallaki Gidan Kaina”: Yar Shekara 19 Ta Baje Kolin Karamin Gidan Da Ta Ginawa Kanta

  • Wata matashiyar budurwa ta garzaya shafin Twitter don nunawa mutane wani karamin gida da ta samawa kanta a shekaru 19
  • Matashiyar, Thaidzo, ta ce tana farin cikin mallakar gida alhalin tana matashiya kuma tana Allah-Allah ta baje kolin gidan
  • Girman gidan da kayayyakin da aka yi amfani wajen gina shi ya haifar da martani daga masu amfani da Twitter

Wata budurwa ta garzaya Twitter domin baje kolin dan karamin gidan da ta ginawa kanta.

Budurwar mai suna Thaidzo, ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta ce a karshe ta zama mai gidan kanta a shekaru 19.

Budurwa ta cika da murnar mallakar karamin gida
“Yanzu Na Mallaki Gidan Kaina”: Yar Shekara 19 Ta Baje Kolin Karamin Gidan Da Ta Ginawa Kanta Hoto: Twitter/@thaidzo7
Asali: Twitter

Thaidzo ta nunawa duniya makullin gidan a daya daga cikin hotunan, wanda ya yadu a yanzu da samu martani a Twitter.

Hotunan dan karamin gida mallakin wata budurwa ya yadu a Twitter

Kara karanta wannan

Yadda Hoton Rahama Sadau Da Wani Farin Fata Ya Haddasa Cece-Kuce a Soshiyal Midiya

An gina gidan ne da kwano maimakon bulo sannan anyi rufin ne da zinki shima kamar dai yadda bangon yake.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Alamu sun nuna daki daya ne a gidan amma dai ba a tabbatar ba domin dai bata nuna ainahin cikin gidan ba.

Sai dai akwai alamar Thaidzo na alfahari da gidan nata duk da kankantarsa da kuma yanayinsa.

Ta rubuta yayin da take wallafa hoton:

"A shekaru 19 na mallaki wuri na kaina."

Kalli wallafarta a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Sinethemba_S ta ce:

"Sannu da kokari Nana. Mutane da dama a nan suna caccakar ki daga bayan dakunan gajiyayyun iyayensu da falon kakanninsu...kada ki yi kasa a gwiwa. Ina maki fatan mallakar wannan filin sannan ki dawo nan da cikakken burinki a kai. Koda baki samu ba, kina da kwanciyar hankali,."

Kara karanta wannan

Matar Da Ta Yi Wa Maza 2 Alkawarin Aure Ta Koka a Ranar Bikinta, Saurayin Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo

@Nonksv ta yi martani:

"Irin wannan wallafar shi na fi so. Yana nuna yarda da kai da girma wanda dandalin soshiyal midiya baya nunawa akai-akai."

@kgonewild21 ta yi martani:

"Nasara nasara ce. Duk kankantar ta. Wannan a nan shine tushen makomar gobe."

@bobbys_wingman ta yi martani:

"Nasara, nasara ce."

Matashi ya kalubalanci mai aikin ginin da ya sha alwashin gina dankareran gida da miliyan 5

A wani labarin, mun ji cewa wani mai aikin gini, Abraham, ya yi wani rubutu da ya yadu a Twitter sannan ya ce zai iya gina hadadden gida kan naira miliyan 5.

A lokacin da ya yi rubutun a twitter, mutane da dama sun garzaya sashinsa na sharhi da ayoyin tambaya da nuna shakku, musamman yanzu da kayan gini suka yi tsada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng