Yanzu Yanzu: Hukumar DSS Ta Maka Godwin Emefiele a Kotu
- Hukumar tsaro ta DSS ta gurfanar da gwamnan babban bankin CBN da aka dakatar, Godwin Emefiele a gaban kotu
- Hakan ya biyo bayan umurnin da babbar kotun Abuja ta ba DSS na gurfanar da Emefiele ko sakinsa cikin mako guda
- Hukumar tsaron farin kayan ta sha alwashin tafiyar da lamarin cikin kwarewa tare da yin gaskiya da adalci a aikinta
Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta gurfanar dakataccen gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele a gaban kotu, jaridar The Cable ta rahoto.
Peter Afunanya, kakakin hukumar DSS ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 13 ga watan Yuli.
A cewar Afunanya, sun dauki wannan matakin ne domin yin biyayya ga hukuncin da babbar kotun da ke zama a babban birnin tarayya ta yanke.A cewar Afunanya, sun dauki wannan matakin ne domin yin biyayya ga hukuncin da babbar kotun da ke zama a babban birnin tarayya ta yanke.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng ta rahoto a cewa wata babbbar kotu ta umurci hukumar DSS da ta maka Emefiele a kotu idan har akwai zargin da take yo a kansa.
Alkalin kotun, Hamza Muazu, ya bukaci rundunar tsaron da ta saki tsohon gwamnan na CBN kan beli idan har ba a kai shi kotu ba cikin mako guda.
Za mu yi aiki cikin kwarewa, DSS yayin da ta gurfanar da Emefiele
Hukumar DSS ta ba jama'a tabbacin gudanar da aikinta cikin kwarewa, tare da yin adalci da gaskiya wajen tafiyar da lamarin.
Sai dai kuma, rundunar tsaron sirrin ta ki bayyana tuhume-tuhumen da take yi a kan Emefiele.
Jaridar Punch ta nakalto sanarwar na cewa:
" wani umurni da babbar kotun ta bayar a yau, 13 ga watan Yulin 2023, saboda haka hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta tabbatar da cewar an gurfanar da Mista Godwin Emefiele a kotu don bin umurnin.
"Jama'a na iya tuna cewa a 2022, hukumar ta nemi izinin kotu na tsare shi a kan wani bincike da ake yi.
"Koda dai ya samu umurnin da ke hana haka daga wata babbar kotun FCT, runduna, ta kama shi a watan Yunin 2023, kan wani laifi mai karfi da ake zarginsa da aikatawa, daya daga cikinsu ne dalilin gurfanar da shi a yanzu."
Shugaban kasa Tinubu ya dakatar da Emefiele
A ranar 9 ga watan Yuni ne Shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele sannan ya bukaci ya mika ragamar ofishinsa ga Folashodun Adebisi Shonubi, mataimakin gwamnan bankin.
Jim kadan bayan nan sai hukumar DSS ta sanar da cewar Emefiele na tsare a hannunta saboda dalilai na wasu bincike da take gudanarwa.
Asali: Legit.ng