"Ban Taba Sanin Zan Zama Shugaban Kasa Ba" Abinda Tinubu Ya Fada Wa Gwamnonin 1999
- Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce bai taba sanin cewa zai zama shugaban kasar Najeriya ba
- Tinubu wanda ya bayyana haka a lokacin da ya karbi bakuncin tsoffin gwamnonin 1999 ya ce Allah ne ya kai shi matsayin da yake kai a yanzu
- Tsohon gwamnan na Lagas ya yi alkawarin samar da tsayayyen wutar lantarki da tabbatar da zaman lafiya da ci gaban Najeriya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa bai taba sanin cewa zai dare kan kujera ta daya a kasar ba, jaridar Daily Trust ta rahoto.
A cewar kakakin shugaban kasar, Dele Alake, Tinubu ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga rukunin gwamnonin 1999 a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Tsoffin gwanonin sun ziyarci fadar shugaban kasa don ganawa da Tinubu, wanda ya kasance gwamnan jihar Lagas daga watan Mayun 1999 zuwa 2007.
Cire Tallafin Mai: Na San Yan Najeriya Na Shan Bakar Wahala Amma A Kara Hakuri, Tinubu Ya Fadi Tanadin Da Ya Yiwa Talakawansa
Shugaban kasar ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Mun yi aiki a matsayin gwamnoni sannan mun zauna a wannan zauren. Kawai abun da nake so shine damokradiyya da ceto kasar. Ban taba tunanin zan kasance a nan a matsayin shugaban kasa ba, amma Allah madaukakin sarki ya kawo ni."
Ya ba tsoffin gwamnonin da yan Najeriya tabbacin cewa zai yi aiki kan "hadin kai, daidaito, zaman lafiya da ci gaban kasar."
"Jajircewana wajen daga darajar damokradiyya ba mai karewa bane. Na ji dadi kan adadinku da kuka zo nan. Ina da budaddiyar manufa. Kune masu bani shawara. Mun shiga tafkin tare sannan muka fafata da wani alade. Mun yi datti, sannan muka tsaftace kanmu. Wannan ne dalilin da yasa na kasance a nan a yau," inji shi.
Tinubu ya dauki alkawarin daidaita wutar lantarki
Da yake bayyana cewa kasar ba za ta samu ci gaba mai ma'ana ba idan ba a gyara wutar lantarki ba, shugaban kasa Tinubu ya ba da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da albarkatun iskar gas, tare da amfani da duk wata dama don tabbatar da samar da tsayayyen wutar lantarki.
Kan tsaro, shugaban kasar wanda ya gana da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno don bitar lamarin tsaro a arewa maso gabas, ya roki yan Najeriya, musamman jihar Filato, da su yi amfani da hanyar sulhu wajen magance rikice-rikice.
Tsoffin gwamnonin sun bukaci shugaban kasar da ya ci gaba da kokarinsa na ganin Najeriya ta samu ci gaba tare da sa himma, dagewa, da juriya, da kuma yarda da goyon bayansu ga manufofin ci gaba, tare da yin alkawarin samar da tsarin zamantakewar da ya dace don cimma manufar.
Tinubu ya gana da tsoffin gwamnonin 1999 a fadar villa
A baya mun ji cewa, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na gana wa yanzu haka da tawagar gwamnonin jihon Najeriya na shekarar 1999 a fadar shugaban ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Tinubu na ɗaya daga cikin mambobin tawagar gwamnonin waɗanda suka hau kan madafun iko karon farko a 1999.
Asali: Legit.ng