Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Na Ganawa Mai Muhimmanci Da Zulum a Fadar Villa

Yanzu Yanzu: Shugaban Kasa Tinubu Na Ganawa Mai Muhimmanci Da Zulum a Fadar Villa

Abuja - Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na ganawa da Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Channels TV ta rahoto.

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gwamnan wanda ya isa fadar villa da misalin karfe 1:00 na ranar Laraba, 12 ga watan Yuli, ya samu tarba daga wajen shugaban ma'aikatan shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.

Zuwa yanzu babu wani cikakken bayani kan abun da ganawar tasu ta kunsa.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng