Gwamnan Rikon Kwarya Na Jihar Ondo Ya Yi Karin Haske Kan Rashin Lafiyar Gwamna Akerdolu
- Gwamnan rikon ƙwarya na jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, ya buƙaci a sanya lura kan batun rashin lafiyar gwamna Oluwarotimi Akeredolu
- A cikin wata sanarwa, Aiyedatiwa ya ce akwai ƙarairayi, gutsiri tsoma da rubuce-rubuce kan rashin lafiyar Akeredolu
- Aiyedatiwa ya bayyana cewa ana yaɗa bayanan ƙarya da nufin kawo ruɗani a jihar musamman a soshiyal midiya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Akure, jihar Ondo - Lucky Orimisan Aiyedatiwa, gwamnan riƙon ƙwarya na jihar Ondo a ranar Talata, 11 ga watan Yuli, ya bayyana cewa ana yaɗa ƙarya da ƙarairayi kan haƙiƙanin halin rashin lafiyar da gwamna Rotimi Akeredolu yake ciki.
Legit.ng ta rahoto cewa Aiyedatiwa ya zama madadin gwamnan ne bayan ya tafi neman magani a ƙasar waje.
'Na yi magana da Akeredolu a ranar Lahadi', cewar Aiyedatiwa
Da yake magana kan rashin lafiyar gwamnan, Aiyedatiwa ya ce ya tattauna da Akeredolu a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli, jaridar The Nation ta rahoto.
Gwamnan Jihar Ondo Ya Kara Wa'adin Hutun Neman Magani Har Sai Baba Ta Gani, An Bayyana Dalilin Hakan
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Aiyedatiwa ya bayyana cewa akwai ƙarairayi, gutsiri tsoma da munanan rubuce-rubuce da ake yi musamman a jaridun takarda da soshiyal midiya domin kawo ruɗani a cikin jihar, rahoton Premium Times ya tabbatar.
Wani ɓangare na sanarwar da ya rattaɓawa hannu na cewa:
"Akeredolu yana cikin kuzari, inda yake samun waraka sannan ana sa ran zai dawo kan kujerarsa ya ci gaba da ayyukan alherin da yake yi a jiha da zarar likitocinsa sun tabbatar da ya warke."
"Ina tuntuɓarsa na baya-bayan nan ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli, lokacin da ya nuna godiyarsa a gare ni da sauran mambobin majalisar zartaswar jihar bisa tafiyar da lamuran jihar da mu ke yi a bayansa."
Haka kuma, Aiyedatiwa ya tabbatarwa da mutanen jihar Ondo cewa babu wani giɓi wurin gudanar da mulki domin ya tsaya kai da fata wajen jan ragamar jihar.
Akeredolu Ya Kara Wa'adin Jinya a Kasar Waje
A wani labarin kuma, gwamnan jihar Ondo ya ƙara wa'adin lokacin da zai kwashe a ƙasar wajen domin neman maganin rashin lafiyar da yake fama da ita.
Rotimi Akeredolu ya ƙara wa'adin neman maganin ne har sai baba ta gani bayan wata ɗayan farko da ya ɗauka ya ƙare.
Asali: Legit.ng