“Ya Ga Rayuwa”: Matashi Ya Fara Gasar Kuka Na Awa 100, Ya Sharbi Kukan Awa 2 Zuwa Yanzu
- Wani mutumi ya fara gasar kuka yayin da ya sha alwashin shafe 100 yana kuka ba tare da tsayawa ba
- Wani bidiyo ya nuno mutumin yana kururuwa kamar wanda aka aikowa sakon mutuwar wani makusancinsa
- Bidiyon ya nuno wani agogo a kan kujera a gefensa, kuma ya nuna ya shafe tsawon awanni biyu yana kuka
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Rahotanni sun kawo cewa wani mutum ya fara abun da ake kira da gasar kuka wanda zai shafe tsawon awanni 100 yana yi.
A wani bidiyo da @cmrinfluencialhub ya wallafa a TikTok, an gano mutamin yana kururuwa kamar an aiko masa da sakon mutuwar wani dan uwansa.
Hakazalika, wani bidiyo da @instablog9ja ya wallafa, an ga mutumin yana kuka da budaddiyar murya kamar wani mugun abu ya faru da shi.
Bidiyon ya nuna cewa ya shafe tsawon awanni biyu yana kururuwa ba tare da tsayawa ba kuma ya ce a shirye yake ya ci gaba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An tattaro cewa yana shirin shiga kundin bajinta na Guinness, amma ba a sani ba idan anyi rijistan gasar kukan a wajen kungiyar.
Hakazalika, binciken Google bai nuna wani ya taba yin irin wannan kasar ba. Ba a kuma tabbatar da ko mutumin dan Najeriya bane, yayin da wasu suka yi hasashen cewa dan Kamaru ne.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@Magicj128:
"Sunansa Danny Green kuma ya fito ne daga kasar Kamaru."
@iamdakejr ta yi martani:
"Najeriya kasata. Saurayin wata."
@JGoldwishbets ta ce:
"Ya kara faaa watakila Allah zai ji tausayin yan Najeriya."
@Irunnia_ ta ce:
"Ban san yadda mutum zai ji da wannan wawancin ba. Yi tunanin kuka na awanni 100. Ba za ka ji ciwon kai mai tsanani ba?"
Matar Da Ta Yi Wa Maza 2 Alkawarin Aure Ta Koka a Ranar Bikinta, Saurayin Ya Hana Ta Zuwa Wajen Daurin Aure a Bidiyo
@temitopepr ta ce:
"Da alama wannan ya ga halin rayuwa."
@TundeJamiu5 ya ce:
"Wai me ke damunmu ne komai daban yake a kasar nan!! kai, muna bukatar sauyin tunani."
Matashi ya fara gasar waka na awanni 200
A wani labarin, mun ji cewa wani dan Najeriya mai suna Oluwatobi Kufeji Àlejòpàtàkì, ya fara rera wakar yabo da gasa a Lagas yayin da yake shirin shiga kundin tarihi na duniya a matsayin mawakin da ya fi kowa dadewa yana rera waka.
A ranar 10 ga watan Yuni, Oluwatobi ya wallafa a Instagram cewa kungiyar ta amince da bukatarsa na shafe tsawon awanni 200 yana rera waka sannan ya sanar da cewar zai kafa tarihi a matsayin mawaki mafi dadewa yana rera waka a nan gaba kadan.
Asali: Legit.ng