Karin Bayani: An ga Tsohon Shugaban Kungiyar ASUU, Dipo Fasina, Da Ya Bata

Karin Bayani: An ga Tsohon Shugaban Kungiyar ASUU, Dipo Fasina, Da Ya Bata

  • Sabon bayani ya nuna cewa an ga tsohon shugaban kungiyar ASUU, Dipo Fasina wanda aka fi sani da Jingo
  • An dai nemi Fasina wanda ya shirya da zumar tafiya kasar Aljeria bisa gayyatar da gwamnatin kasar ta yi masa an rasa
  • Sai dai kuma a yanzu hukumar kula da yan Najeriya mazauna kasashen waje ta tabbatar da ganinsa

Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu haka sun tabbatar da cewar an ga fitaccen malamin Najeriya kuma tsohon shugaban kungiyar malaman jami’o’i (ASUU), Dipo Fasina, wanda aka fi sani da ‘Jingo'.

Da farko dai an samu labarin rashin ganin Jingo wanda aka ce ya bata tun a ranar Asabar 1 ga watan Yuli, kamar yadda jaridar Premium Times ta rahoto.

An tattaro cewa mista Fasina mai shekaru 76 zai je kasar Aljeria bisa gayyatar da gwamnatin Algeria ta yi masa lokacin da jirgin da zai dauke shi daga Istanbul, kasar Turkiyya ya wuce ya bar shi.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Motar da ta dauko masu zuwa 'party' ta yi karo da motar yashi, mutum 20 sun mutu

Tsohon shugaban ASUU ya bata
Yanzu Yanzu: Tsohon Shugaban Kungiyar ASUU, Dipo Fasina, Ya Bata Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Da farko mun ji cewa hugabar hukumar da ke kula da yan Najeriya mazauna waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta tabbatar da lamarin ga jaridar Premium Times.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Dabiri-Erewa ta ce hukumarta na sane da lamarin kuma "muna aiki a kansa."

An gano Farfesa Fasina wanda ya bata a kasar Turkiyya

Sai dai kuma a sabuwar sanarwa da hukumar NIDCOM ta fitar a shafinta na Twitter, ta tabbatar da ganin Farfesan wanda ya bata a birnin Instabul na kasar Turkiyya.

Hukumar ta rubuta a shafinta:

“Hukumar yan Najeriya mazauna kasashe waje tare da hadin gwiwar hukumar Najeriya a kasar Turkiyya sun yi nasarar gano Farfesa Fasina da ya bata na yan kwanaki a filin jirgin saman Istanbul a lokacin da ya ke shiga jirgi don komawa gida.
"Mista Fasina mai shekaru 76, yana hanyarsa ta zuwa kasar Algeria ne, sai jirgin da zai sada shi da kasar daga Istanbul na kasar Turkiyya ya tafi ya barsa.

Kara karanta wannan

Dakyar: Bayan shan titsiyen kwanaki a hannun DSS, tsohon gwamnan Arewa ya shaki iskar 'yanci

"Babban godiya ga jakadan Najeriya a kasar Turkiyya wanda nan take ya tura jami'ai zuwa filin jirgin domin gano inda yake a filin jirgin saman Istanbul mai cike da cunkoson jama’a."

Ana kokarin ganin ya dawo gida cikin koshin lafiya

Mun dai kuma kawo a baya cewa abokai da hadiman malamin da ya bata da dama ciki harda kungiyoyi kamar su ASUU da JAF na kokarin ganin ya dawo cikin koshin lafiya.

Da yake zantawa da jaridar a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuli, shugaban ASUU, Mista Osodeke, wanda ya kasance Farfesa ya ce kungiyar na aiki tukuru don tabbatar da inda jigonta yake da kuma tabbatar da ganin ya dawo lafiya.

"Eh muna sane da ci gaban kuma muna aiki a kansa, don haka idan muka kammala nan da yan kwanaki biyu zuwa uku za mu sanar da ku," inji Mista Osodeke a wayar tarho.

Wani makudancin Mista Fasina wanda baya so a ambace shi ya bayyana lamarin a matsayin na kashin kai, ya tabbatar da cewar akwai yiwuwar su yi tafiya nan ba da jimawa ba don nemansa.

Kara karanta wannan

Hajiya Halimatu Attah: Fasinjar Jirgin Kasan Kaduna-Abuja Mafi Tsufa Da Aka Yi Garkuwa Da Ita Ta Rasu

Majiyar ta ce:

“Hakika wannan lamari ne na kashin kai ba na kafafen yada labarai ba. Muna aiki don dawo da shi kuma zai kasance cikin koshin lafiya. Watakila zan yi tafiya kowane lokaci daga yanzu don dawo da shi."

Halimatu Attah: Fasinjar da ta fi kowa tsufa a jirgin kasan Abuja-Kaduna da aka kaiwa hari bara ta kwanta dama

A wani labari na daban, mun ji cewa matar nan da ta fi kowa tsufa cikin fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna 63 da yan ta'adda suka yi garkuwa da su a ranar 28 ga watan Maris din 2022, ta rasu tana da shekaru 85 a duniya.

Hajiya Halimatu Attah ta rasu a ranar Laraba, 5 ga watan Yuli da misalin karfe 6:20 na yamma a Kaduna kamar yadda wani danginta ya bayyana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng