Yan Sanda Sun Kama Mutumin Da Ake Zargi Da Sakin Hotunan Tsaraicin Tsoffin Yan Matansa
- Rundunar yan sandan jihar Lagas ta yi nasarar damke wani mutum da ake zargi da yada hotuna marasa kyau
- Amarah Kennedy dai na yada hotunan tsaraici na tsoffin yan matansa domin karbar kudade daga hannunsu
- Kamar yadda wata majiya mai tushe ta sanar, ana gab da gurfanar da matashin wanda ke tsare a hannun hukuma
Lagos - Channels TV ta rahoto cewa yan sanda sun kama wani mutum mai suna Amarah Kennedy, wanda aka zarga da yada hotunan tsaraicin tsoffin yan matansa a jihar Lagas.
Wata majiya mai tushe a rundunar ofishin jihar ta bayyana cewa mutumin na tsare a sashin kare jinsi na hedkwatar runudnar yan sandan a Lagas.
Jaridar Blueprint ta kuma rahoto cewa daya daga cikin yan matan da mutumin ya saki hotunan tsaraicinsu mai suna Kester, ta tabbatar da kamun nasa ga manema labarai a ranar Juma'a.
Za a gurfanar da Amarah Kennedy
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An kuma tattaro cewa za a gurfanar da wanda ake zargin nan da dan lokaci kadan.
A cewar majiyar yan sandan da ke kusa da binciken, Kennedy ya yi soyayya da wasu mata wadanda ya mallaki hotunan tsaraicinsu sannan ya yi amfani da su wajen karbar kudi daga hannunsu ta hanyar yi masu bita da kulli.
Majiyar ta ce:
"A lokacin da suka daina tura masa kudi, sai ya tura wa wani hoton a Facebook.
"Zai je shafin Facebook din budurwar sannan ya aika daya daga cikin hotunan ga abokanta. Idan ta gani, sai ta gaggauta aika masa da kudi.
"Ya ci gaba da yin haka har sai da ya tura a kungiyar cocin wata bazawara na Whatsapp. Ya kuma aike hoton ga surukan marigayi tsohon mijin matar."
An tattaro cewa biyu daga yan mata 10 da Kennedy ya yi wa haka ne kawai suke shirin bibiyar shari'a da shi.
Yan sanda na neman mutumin da ya yada hotunan tsaraici na wata bazawara
A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar 'yan sandan jihar Legas ta buƙaci wani ɗan kasuwa, Amarah Kennedy, ya hanzarta miƙa kansa ya yi bayanin da zai gamsar cewa ba shi da hannu a yaɗa Hotunan tsiraici.
Hukumar 'yan sanda ta yi kira ga ɗan kasuwan ya gaggauta zuwa ya yi bayani kan zargin da ake masa na yaɗa Hotunan tsiraicin wata bazawara a soshiyal midiya.
Mai magana da yawun hukumar 'yan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a sahihin shafinsa na Tuwita ranar Laraba.
Asali: Legit.ng