Karshen Kyau: Budurwa Ta Gigiza Intanet da Bidiyon Santala-Santalan Kawayenta

Karshen Kyau: Budurwa Ta Gigiza Intanet da Bidiyon Santala-Santalan Kawayenta

  • Wani bidiyo da wata budurwa ta wallafa wanda ya nuna kyawawan ƙawayenta a cikin kayan makaranta ya ja hankali a soshiyal midiya
  • Bidiyon ya nuna yadda santala-santalan matan suka sanya fararen hijabai kuma suna yi wa kamarar da ke ɗaukarsu murmushi
  • Duk da sun sanya Hijabai iri ɗaya amma kyaun fuskokinsu ya nuna suna cikin farin ciki da nishaɗi

Wani bidiyon ƙawayen juna wanda ya ɗauki Hotunan kyawawan 'yan matan na ajin farko a makaranta ya girgiza mutane a soshiyal midiya.

Bidiyon ya nuna cauɗa-cauɗan matan waɗanda suka sanya Hijabai farare iri ɗaya da kayan makarantarsu, suna masu yin murmushi yayin da kamara ke ɗaukarsu.

Hoton kyawawan mata uku.
Karshen Kyau: Budurwa Ta Gigiza Intanet da Bidiyon Santala-Santalan Kawayenta Hoto: @marhyermih
Asali: TikTok

Ɗaliban makarantar sakandiren mata cikin shiga mai tsafta

Duk da 'yan matan sun sanya kallabi iri ɗaya amma kyaun da Allah ya yi wa matan ya fito fili a fuskokinsu, ga shi sun nuna suna cikin farin ciki da nishaɗi.

Kara karanta wannan

Uwar Gida da Mata Ta 2 Sun Kai Wa Mijinsu Sabuwar Amaryar da Ya Auro, Bidiyon Ya Girgiza Jama'a

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mafi akasarin masu amfani da kafafen sada zumunta da suka kalli bidiyon sun tabbatar da cewa Allah ya yi wa 'yan matan kyau na gani na faɗa.

Haka nan kuma da yawan waɗanda suka kalli bidiyon sun musu Addu'ar Allah ya ba su mazajen aure masu kirki da hali mai kyau.

Zuwa yanzun da muke haɗa muku wannan rahoton, mutane sama da 30,000 suka kalla kuma sama da 100 sun yi sharhi kansa.

Kalli bidiyon kyawawan 'yan mata cikin shiga mai tsafta

Wasu daga cikin martanin mutane game da bidiyon kyawawan 'yan matan

@Ashaer4747848 ya ce:

"Asma'u tana da kyau sosai."

@Zaharaventures ya maida martani da cewa:

"Dukkan ku Allah ya muku kyaun halitta, ina rokon Allah mai girma da ɗaukaka ya zaɓa muku mazan aure na gari, masu hali da ɗabi'a mai kyau."

Kara karanta wannan

Sabon Gwamnan PDP Ya Sanar Da Rage Kudin Makaranta Da Kashi 50 A Jami'ar Jiharsa

@Illiyarzakari ya ce:

"Fateema tana kyau sosai da sosai."

@anwarayuba ya ce:

"Maman farhan ta fi sauran kyau, muna rokon Allah ya baku miji na gari kuma ya baku lafiya da farin cikin a rayuwarku."

"Ba Zan Karɓa Ba Sai Kin Duƙa" Miji Ya Umarci Matarsa a Bidiyo, Ya Ki Karban Abinci

A wani labarin na daban kuma Wata mata 'yar Najeriya ta sha mamaki yayin da habibinta ya umarci ta durkusa kafin ya karɓi abincin da ta kawo masa.

Magidancin ya gaya mata cewa shi ɗan gargajiya ne kuma ya zama dole ta duƙa kan guiwowinta idan zata ba shi abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262