Shugaba Tinubu Ya Shafe Harajin da Aka Lafta, Ya Ƙirƙiro Dokokin Rage Raɗaɗi

Shugaba Tinubu Ya Shafe Harajin da Aka Lafta, Ya Ƙirƙiro Dokokin Rage Raɗaɗi

  • Bola Ahmed Tinubu ya shigo da wasu sababbin dokoki hudu da su ka shafi gyaran tattalin arziki
  • Shugaban kasan ya yi fatali da harajin 5% da ya kamata a rika karba daga kamfanonin sadarwa
  • Ganin halin da ake ciki, Dele Alake ya ce Tinubu ba zai kara haraji ba tare da ya tuntubi al’umma ba

Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a kan wasu dokoki a Najeriya. Hakan ya jawo janye harajin 5% kan kamfanonin sadarwa.

Tashar Channels ta ce Mai ba shugaban kasa shawara wajen harkoki na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake ya shaidawa manema labarai haka.

Da yake magana da ‘yan jarida a fadar shugaban kasa da ke birnin Abuja, Mista Alake ya ce Bola Tinubu ya cire harajin da aka laftawa wasu kayayyaki.

Kara karanta wannan

Tsohon Shugaban Hukumar NUC Ya Fadi Dalilin Rubuta Murabus, Ya Ajiye Mukaminsa

Shugaba Tinubu
Bola Tinubu da wakilan bankin Amurka Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar da ta dage lokacin fara aiwatar da wasu sauye-sauyen da aka yi a kan tattalin arziki zuwa Satumba a maimakon Mayu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda dokar haraji ta 2017 tayi tanadi, Alake ya ce an kara tsawon watanni uku ne domin ankarar game da canjin da za a samu wajen karbar haraji.

An janye dokar kwastam

Tashar ta rahoto Mai magana da yawun shugaban kasar ya na cewa Tinubu ya shigo da dokar kwastam da ta canza lokacin fara dabbaka sabon tsarin haraji.

Mai girma ya bada umarnin dakatar da karin haraji kan robobi da kwalabe, sannan an tsaida canza kudin da ake karba wajen shigo da wasu abubuwan hawa.

Tribune ta rahoto Alake yana cewa shugaban kasa ya kawo wadannan dokoki ne saboda lura da yadda ‘yan kasuwa da talakawa su ke kokawa da haraji.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Sa Labule da Tsohon Ministan Buhari a Villa, Yan Najeriya Sun Nuna Damuwa

Haraji sun yi yawa

Hadimin ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya za ta dauki mataki game da yawan harajin da ake laftawa a Najeriya, wadanda su ke takurawa ‘yan kasuwa.

Gwamnatin Tinubu ta dauki alkawarin za a kawo tsare-tsare da za su jawo a ji dadin kasuwanci.

Mista Alake ya sanar da al’ummaShugaba Tinubu ba zai taba kara haraji ba tare da ya tuntubi jama’a ba, sannan ba za a bari a sabawa tsarin tattalin arziki ba.

Yadda Pantami ya yaki karin harajin

A lokacin da aka ji Gwamnatin tarayya ta na tunanin karbar haraji na 5% daga duk wani kamfanin sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami bai yarda da hakan ba.

Sa'ilin ya na Ministan sadarwa, an ji labari Isa Pantami ya yi kokarin ganin ba a kara harajin ba, kusan hakan ya jawo sabani tsakaninsa da ma'aikatar kudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Tags: