Kotu Ta Tura Matashi Mai Shekaru 32 Gidan Yari Bisa Laifin Datsewa Abokinsa Hannaye a Bauchi

Kotu Ta Tura Matashi Mai Shekaru 32 Gidan Yari Bisa Laifin Datsewa Abokinsa Hannaye a Bauchi

  • Kotu ta tura matashi Auwal Usman, mai shekara 32 gidan yari, bisa laifin datsewa abokinsa hannu a Bauchi
  • Matashin ya aikata wannan ɗanyen aiki ne biyo bayan saɓani da ya samu da abokinsa Sabo Abduwa, wanda hakan ya sa suka kacame da faɗa
  • Ana cikin faɗan ne Usman ya zaro adda, wacce ya yi amfani da ita wajen sare hannayen abokin nasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Bauchi - Kotun Majistare ta jihar Bauchi ta ɗaure wani matashi mai suna Auwal Usman, ɗan shekara 32 bisa samunsa da laifin amfani da adda wajen datse duka hannayen abokinsa.

Alkalin kotun, Haruna Abdulmimini Mamman, ya samu Usman da laifin yankewa abokinsa hannuwa da adda a lokacin da suka yi faɗa tsakaninsu kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Kotu ta tura matashin da ya sarewa abokinsa hannu gidan yari
Kotu ta tura matashin ya datsewa abokinsa hannu a Bauchi gidan yari. Hoto: The Punch
Asali: UGC

Abinda ya janyo matashin ya datsewa abokinsa hannaye 2

Kara karanta wannan

Bayan Ya Kwanta da Ita, Wani Ɗan Kasuwa Ya Saki Hotuna 50 Na Tsiraicin Wata Mata, Ya Shiga Matsala

Jami'i mai shigar da ƙara, Yusuf Musa, ya shaidawa kotun cewa, wanda ake zargin mazaunin ƙauyen Dogon Ruwa da ke Ari, a karamar hukumar Ningi ta jihar Bauchi ne.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya bayyana cewa ya samu rashin jituwa ne tsakaninsa da abokinsa mai suna Sabo Abduwa wanda har abun ya ka su ga yin faɗa.

Musa ya ƙara da cewa a yayin da suke faɗan ne Usman ya zaro adda, sannan ya yi amfani da ita wajen datse hannayen abokin nasa biyu.

A take hannu ɗaya ya faɗi ƙasa a yayin da ɗayan kuma ya riƙa lilo saboda wata fata da ta riƙe shi.

Musa ya kara da cewa, an garzaya da Abduwa zuwa babban asibitin Ningi, inda aka yanke ɗayan hannun da ya rage domin ceto rayuwarsa daga munanan raunukan da ya samu.

Kara karanta wannan

Dalibin Jami'a Da Ke Wankin Mota Ya Yi Bayanin Dalilinsa Na Kama Sana'ar Gadan-gadan

Matashin da ake zargi ya amsa laifin sarewa abokin nasa hannaye

Da aka karantawa wanda ake zargin tuhume-tuhumen da ake yi masa, ya amince da aikata su amma ya roki kotu da ta yi masa sassauci, saboda a cewarsa wannan ne karo na farko da ya yi irin hakan.

Da yake yanke hukunci, Abdulmumini Mamman, ya ce kotun ta gamsu cewa Abduwa ya rasa hannayensa biyu ne sakamakon wannan mugun aiki da wanda ake zargin ya aikata masa, wanda kuma zai sa shi nakasa ta har abada.

Don haka Mamman ya yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan gyaran hali ba tare da zaɓin biyan tara ba saboda ɗanyen aikinsa da ya Saɓawa sashe na 241 na kundin laifuffuka.

Ya kuma umarce shi da ya biya Abduwa kuɗaɗe naira 150,000 da zai yi amfani da su wajen jinya kamar yadda Leadership ta wallafa.

Dan majalisan Bauchi ya rasu kwanaki uku kafin ƙarewar wa'adinsa

Kara karanta wannan

Ana Shagalin Babbar Sallah, Gwamna Ya Dakatar da Wasu Ma'aikata da Babban Shugaba Nan Take

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan wani ɗan majalisar dokokin jihar Bauchi, Ado Wakili da ya rasu ana saura kwanaki uku wa'adin mulkinsa ya ƙare.

Kafin rasuwarsa, Ado Wakili shi ne ɗan majalisar da ke wakiltar mazaɓar Burra a zauren Majalisar Dokokin jihar Bauchi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng