Gwamnatin Ekiti Ta Hana Gasar Kiss Na Kwanaki 3 Da Ake Shirin Yi, Ta Gargadi Kungiyar Masu Otal
- Gwamnatin Ekiti ta dauki tsatsauran mataki a kan wadanda ke shirin kafa sabon kundin tarihi na duniya a jihar
- Gwamnatin jihar karkashin jagorancin Biodun Oyebanji ta soke "gasar kiss" wanda ake yi wa lakabi da “kiss-a-thon” a jihar sannan ta haramta irin wannan abu a jihar
- A halin da ake ciki, gwamnatin ta kuma sanar da haramta gasar da aka shirya sannan ta ce za a hukunta duk wurin da ya karbi bakuncin wannan taro
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ekiti - Gwamnatin jihar Ekiti ta haramta gasar kiss na kwanaki uku da ake shirin yi wanda ake yi wa lakabi da “Kiss-a-Thon”.
Gasar wanda aka shirya farawa a ranar Juma'a, 7 ga watan Yuli, zai shafe tsawon kwanaki uku ana yinsa a jihar.
Gwamnatin Ekiti ta hana "gasar kiss" a jihar
A wani sabon ci gaba, gwamnatin Ekiti ta gargadi kungiyar masu otal a jihar kan irin wannan lamari, Sahara Reporters ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wani talla da ke yawo a jihar da soshiyal midiya, wata kungiya mai suna Sugartee ta shirya gudanar da 'gasar kiss' mafi tsawo wanda za a fara a ranar 7 ga watan Yuli a sanannen wajen wasan nan da ke babban birnin jihar.
Sai dai kuma, a wata wasika zuwa ga sakataren kungiyar masu otal na jihar Ekiti dauke da sa hannun Adelusi A. L, a madadin sakataren dindindin na ma'aikatar al'adu da yawon bude ido, Dele Ogunsemoyin, gwamnatin ta gargadi masu otal kan irin wannan aiki na rashin tarbiya.
"Gasar Kiss-A-Thon", a matsayin taro ba wai rashin dacewa, rashin tarbiya da bata sunan jihar kawai zai yi ba, taro ne da ya saba darajar mutanen jihar sannan zai iya kawo koma baya ga tarbiyan matasanmu," inji sanarwar.
Jihar Ekiti ta gargadi kungiyar masu otal
Sanarwar ta kara da cewa:
"Saboda haka, ma'aikatar al'adu da yawon bude ido ta haramta karbar bakuncin irin wannan taro ko wasu taruka makamancinsa a kowani wuri da ke son ci gaba da aiki bisa doka a jihar Ekiti."
Masu shirya taron sun yi ikirarin cewa an shirya taron ne a kokarin shiga kundin tsari na duniya na gasar kiss mafi tsawo.
Budurwa ta mari kan wani matashi a motar haya, ya fasa mata waya a bidiyo
A wani labarin kuma, an sha yar dirama a wata motar kasuwa bayan wata matashiya ta mari kan wani mutum da bata sani ba.
Kamar yadda budurwar ta bayyana, wata kawarta ce ta ce idan ta isa ta aikata hakan, inda ita kuma ta biye mata.
Asali: Legit.ng