Bayan Shafe Watanni 4 a Otel Din Alfarma, Matashi Ya Ajiye Cak Na Bogi Sannan Ya Tsere

Bayan Shafe Watanni 4 a Otel Din Alfarma, Matashi Ya Ajiye Cak Na Bogi Sannan Ya Tsere

  • Matashi ya yi sojan gona a matsayin ma'aikacin masarautar Abu Dhabi kuma ya zauna a otal din Leela Palace da ke Delhi na tsawon watanni hudu
  • Ya tsere daga otel din ba tare da ya biya bashin fiye da naira miliyan 15 da ake binsa ba sannan ya sace wasu kayayyaki daga dakinsa
  • Yan sanda suna tuhumar mutumin kan laifin zamba da kuma sata sannan sun fara farautar mutumin

An zargi wani matashi da ya yi sojan gona a matsayin ma'aikacin masarautar Abu Dhabi da yaudarar babban otel din alfarma a Delhi da kuma sace masu wasu kayayyaki.

Yan sanda na neman mutumin wanda ya bar otel din bayan ya shafe tsawon watanni hudu a ciki ba tare da ya biya bashin sama da naira miliyan 15 ba, jaridar Independent ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yariman Bakura Ya Sanya Labule Da Shugaba Tinubu, Ya Nemi Wata Alfarma 1 a Madadin 'Yan Bindiga

Matashi ya tsere daga otel
Bayan Shafe Watanni 4 a Otel Din Alfarma, Matashi Ya Ajiye Cak Na Bogi Sannan Ya Tsere Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Ya yi ikirarin cewa shi ma'aikacin masarautar Abu Dhabi ne

Mutumin mai suna Mohammed Sharif, ya shiga Otel din Leela Palace a ranar 1 ga watan Agustan 2022 sannan ya ci gaba da zama a dakin mai lamba 427 har zuwa ranar 20 ga watan Nuwamban 2022.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi ikirarin cewa Sheikh Falah Bin Zayed Al Nahyan, dan gidan sarautar Hadaddiyar Daular Larabawa yake yi wa aiki, sannan ya nunawa ma'aikatan otel din wani katin kasuwanci na bogi da katin shaidar zama a UAE.

Ya kuma biya wani bangare na kudin a watan Agusta da Satumba 2022, amma jimlar kudin da ake binsa ya kai naira miliyan 15.

Ya baiwa otel din cak din naira miliyan 13, wanda ya koma a lokacin da otel din ya yi kokarin cire shi a ranar 22 ga watan Satumban 2022.

Kara karanta wannan

“Matata Bata Sona”: Magidanci Da Bashi Ya Yi Wa Katutu Ya Koka Yayin da Matarsa Ta Daina Yi Masa Magana Kan Ragon Sallah

Ya tafi ba tare da ya sanar da kowa ba

Hukumar oten din sun gano cewa ya bar otel din ba tare da ya sanar da kowa ba.

Sannan sun kuma gano cewa ya sace wasu abubuwa daga cikin dakin da yake masaukinsa.

Otel din ya shigar da kara ofishin yan sanda a ranar Asabar, yana mai tuhumar Mista Sharif da aikata zamba da sata.

An fara farautarsa

Rundunar yan sanda ta shigar da kara a kansa sannan ta fara kokarin gano inda yake.

Suna kuma duba bidiyon CCTV daga otel din da sauran majiyoyi domin samun haske kan ko wanene shi da kuma inda yake.

"Mun kafa wasu tawaga domin kama wanda ake zargin. Ba mu tabbatar da aikinsa kuma muna kokarin samun bayani a kansa," inji wani jami'in dan sanda.

An Turo Wa Wani Mutumi Sama da Biliyan N24bn a Asusun Banki

A wani labari na daban, wani matashi mai suna Joel Julien daga Trinidad ya shiga hannun jami'an tsaro bisa zargin sace makudan kudi daga bankinsa bayan tafka babban kuskure.

An tura ma mutumin kudi sama da biliyan N24bn bisa kuskure a asusunsa amma ganin tamkar ya tsinci dami a kala, mutumin ya ci gaba da sha'aninsa da kuɗin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng