“Ta Yi Kama Da Shi”: Budurwa Ta Saki Bidiyon Wata Tsohuwa Mai Kama Da Bola Tinubu
- Wata matashiya yar Najeriya ta wallafa bidiyon wata tsohuwa wacce ta ce tana kama da shugaban kasa Bola Tinubu
- Matashiyar, Princess Jim, ta wallafa bidiyon a TikTok kuma nan da take ya haddasa cece-kuce tsakanin yan Najeriya
- An gano matar a wani wuri mai kama da kasuwa, inda take kokarin siyan kaya
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata yar Najeriya ta saki wani bidiyo da ke nuna wata mata wacce tace tana kama da shugaban kasa Bola Tinubu.
Matashiyar mai suna Princess Jim, ta wallafa bidiyon a TikTok, tana mai bayyana yadda matar da shugaban kasar suke kama da juna.
A cikin bidiyon, an gano matar sanye da doguwar riga da bai kai kasa da takalminta na silifas.
Bidiyon tsohuwa da ke kama sa Tinubu ya yadu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, ta sanya madubin ido da bakin hula mai kama da raga a kanta.
An gano ta a kasuwa inda take duba wasu kayayyaki.
Matashiyar ta yarda cewa matar na kama da shugaban kasa Tinunu, duba ga kamanninta.
Hakazalika, wasu masu amfani da TikTok sun yarda cewa matar na kama da shugaban kasar sosai.
Sai dai kuma wasu sun soki matashiyar a sashin sharhi, suna tambayar dalilinta na sakin bidiyon matar.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@tamaryakubu25 tace:
"Mamata ta je kasuwa sai ku je kuna daukarta bidiyo."
@CandyAmaa ta yi martani:
"Uwar wani."
@Franklin Ezekiel ya ce:
"Na rantse suna kama lol."
@queen bella ta yi martani:
"babu abun da za ku fada mani na yarda. Jagaban ne wannan."
@Temini’s Fragrance ta ce:
"Kun cika son mugun wasa."
@Jsmart ta ce:
"Kun cika wasa a dandalin nan."
Shugaban kasa Tinubu bai fadi ba wajen duba ofishin mai ba kasa shawara kan tsaro, bincike
A wani labari na daban, wani binciken kwakwaf da aka yi kan wani bidiyo da ke yawo a soshiyal midiya wanda ke ikirarin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya fadi a Abuja ba gaskiya bane.
Wani bidiyo dai ya bayyana a Facebook tare da ikirarin cewa Shugaban kasa Tinubu ya yi tuntube sannan ya fadi a wajen duba sabon ofishin mai ba kasa shawara kan lamarin tsaro. Sai dai baby wani wuri da ke nuna haka a bidiyon.
Asali: Legit.ng