Binciken Gaskiya: Shugaban Kasa Tinubu Bai Fadi Ba Yayin Rangadi a Abuja
- Wani ikirari da ake yi cewa shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya fadi yayin duba sabon ofishin mai ba kasa shawara kan tsaro ba gaskiya bane
- Hatta bidiyon da aka wallafa tare da wannan ikirari bai nuna inda shugaban kasa Tinubu ya yanke jiki ya fadi ba
- Wani cikakken bidiyon ziyarar da Tinubu ya kai ofishin ONSA wanda shahararriyar kafar watsa labaran kasar Channels TV ta daura a YouTube ya tabbatar da bai fadi ba
FCT, Abuja - Wani rubutu da ya karade dandalin Facebook ya yi ikirarin cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya fadi yayin duba sabon ofishin mai ba kasa shawara kan lamarin tsaro (ONSA) a ranar 5 ga watan Yunin 2023.
Rubutun na kunshe da wani bidiyo mai tsawon sakanni 20 na Tinubu da masu tsaronsa suna tunkarar kujerarsa a a cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa, Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.
Yana dauke da rubutu kamar haka:
"Dirama yayin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, GCFR ya fadi a ofishin mai ba kasa shawara kan harkar tsaro ONSA a yau."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Saboda wannan, Africa Check, wani dandalin binciken gaskiya, ya gudanar da binciken kwakwaf.
Lafiyar Bola Tinubu
An rantsar da Tinubu a matsayin shugaban kasar Najeriya a ranar 29 ga watan Mayun 2023. Lafiyarsa shine babban abun damuwa a lokacin zaben, inda masu adawa suka ce bai da isasshen lafiyar da zai jagoranci kasar.
Wannan ikirari ya bayyana a wasu shafukan Facebook da Twitter.
A'a, Shugaban kasa Bola Tinubu bai fadi ba
Bidiyon da aka wallafa a Facebook bai nuna inda Shugaban kasa Tinubu ya fadi ko ya ji tuntube ba a ko'ina.
Wani cikakken bidiyon ziyarar da Tinubu ya kai ofishin ONSA, wanda Channels TV ta wallafa a YouTube ma bai nuna hujjar cewa ya fadi ba.
Abun da Tinubu ya fada mana a Asorock, Ribadu
A wani labarin kuma, mun ji cewa mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu ya bayyana abubuwan da suka tattauna lokacin da su ka hadu da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
A ranar Litinin ne Malam Nuhu Ribadu ya ce sun yi amfani da damar da su ka samu wajen godewa shugaban kasa.
Asali: Legit.ng