Ministan Birnin Tarayya Abuja Na Farko, Ajose-Adeogun, Ya Mutu Yana da Shekara 96
- Ministan babban birnin tarayya Abuja na farko bayan an kafa ta a 1976, Chief Mabolaji Ajose-Adeogun, ya riga mu gidan gaskiya
- Mamban iyalan gidan marigayin, Oluremi Ajose-Adeogun, ya ce tsohon ministan ya rasu ne ranar Asabar 1 ga watan Yuni, 2023
- Tsohon ministan ya ba da gagarumar gudummuwa wajen bunƙasa birnin tarayya kuma ya riƙe mukamai a ɓangaren mai da gas a Najeriya
Ministan birnin tarayya Abuja na farko a tarihin Najeriya, Chief Mobolaji Ajose-Adeogun, ya riga mu gidan gaskiya.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa Chief Ajose-Adeogun ya mutu yana da shekaru 96 a duniya.
Ɗaya daga cikin iyalan gidan marigayin, Oluremi Ajose-Adeogun, shi ne ya tabbatar da haka, inda ya ce tsohon ministan ya rasu ne ranar Asabar, 1 ga watan Yuli, 2023.
Taƙaitaccen tarihin tsohon ministan
Marigayin kwararre ne kuma ya yi aiki a bangaren mai da Gas a Najeriya kuma ya ba da gudummuwa mai girma da ba za'a taɓa manta wa da ita ba a ɓangaren da Najeriya ta dogara shi a matsayin hanyar samun kuɗin shiga.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ba da gudummuwa da kwakwalwarsu wajen tsara birnin tarayya Abuja, kuma shi ne mutum na farko da ya zama Ministan Abuja.
Chief Ajose-Adeogun ya yi aiki a kamfanin haƙo mai Shell (Shell Petroleum Development Company) kuma ya kai matsayin kwamishinan tarayya mai kula dda fannin kwangila da wadatar da mai.
Bayan haka kuma mamacin ya zauna a kujerar kwamishinan ayyuka na musamman a ma'aikatar raya birnin tarayya Abuja yana dab da yin ritaya.
Daga baya kuma bayan kafa birnin tarayya a shekarar 1976, Chief Ajose-Adeogun, ya zama Ministan Abuja na farko a tarihi.
Rahotanni sun bayyana cewa tsohon ministan ya rasu ya bar 'ya'ya da jikoki harda tattaɓa kunne, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Mutane Sun Ɓalle da Sabuwar Zanga-Zanga a Birnin Tarayya Abuja, Sun Faɗi Buƙatunsu
A wani rahoton na daban kuma Mazauna rukunin gidajen Trademore sun ɓalle da zanga-zanga a birnin tarayya Abuja ranar Litinin 3 ga watan Yuli, 2023.
Mazauna Anguwar Trademore da ke kan titin Lugbe zuwa filin jirgin sama sun fara wannan zanga-zanga ne yayin da ma'aikatar Abuja ta fara shirin rushe gidajen yankin.
Asali: Legit.ng