Mazauna TradeMore Sun Balle da Zanga-Zanga a Abuja Kan Yunkurin Rusau
- Mazauna rukunin gidajen Trademore sun ɓalle da zanga-zanga a birnin tarayya Abuja ranar Litinin 3 ga watan Yuli, 2023
- Sun yi kira ga ma'aikatar Abuja ta sauya tunani kan yunkurinta na rushe gidajen Trademore bayan mummunar ambaliyar da ta auku
- A cewarsu, rushe gidajen ba shi ne mafita ba, kamata ya yi a samo kwararrun injiniyoyi su faɗi hanyar kare aukuwar ambaliya nan gaba
FCT Abuja - Mutanen da ke zama a rukunin gidajen Trademore Estate a birnin tarayya Abuja sun fantsama kan tituna suna zanga-zanga kan yunkurin rushe gidajensu.
Jaridar Punch ta rahoto cewa mazauna Anguwar Trademore da ke kan titin Lugbe zuwa filin jirgin sama sun fara wannan zanga-zanga ne yayin da ma'aikatar Abuja ta fara shirin rushe gidajen yankin.
Wannan yunƙurin na zuwa ne bayan mummunar ambaliyar ruwan da ta auku a rukunin gidajen sakamakon mamakon ruwan saman da ya sauka da safiyar Jumu'a, 23 ga watan Yuni.
Idan zaku iya tunawa, ma'aikatar babban birnin tarayya Abuja, FCTA ta ayyana gidajen Trademore da yanki mai cike da haɗari.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar FCTA, ta yanke rushe rukunin gidajen saboda barazanar sake ambaliya a kai a kai a yankin, kuma ta roƙi duk wanda ke zaune ya tattara kayansa ya sauya wuri.
Meyasa suka zabi fitowa zanga-zanga?
Sai dai da safiyar Litinin, 3 ga watan Yuli, 2023, mazauna wannan yanki watau Trademore, suka fito zanga-zangar nuna adawa da matakin da FCTA ke shirin ɗauka.
Masu zanga-zangar sun yi kira ga mahukuntan Abuja cewa maimakon rusau, kama ta ya yi ma'aikatar ta lalubo hanyar warware matsalar daga kwararrun injiniyoyi.
Channels tv ta tattaro cewa masu zanga-zangar sun ɗaga allunan isar da saƙo da aka yi rubutu daban-daban domin jawo hankalin FCTA ta canja tunani.
Wasu daga cikin an rubuta, "A nemi injiniyoyin da zasu lalubo hanyar warware matsalar maimakon bin bakin hanya," "A kawo karshen kashe-kashen rashin imani," "Gidajen Trademore ba su shiga haɗari ba," da sauransu.
Ortom Ya Musanta Rahoton Cewa Shugaba Tinubu Ya Nada Shi a Matsayin Minista
A wani labarin na daban kuma Tsohon gwamnan jihar Benuwai na PDP ya karyata jita-jitar cewa Tinubu ya masa tayin muƙamin Minista.
Rahoton wanda ya karaɗe soshiyal midiya ranar Alhamis ya yi ikirarin cewa Ortom ya shiga jerin Ministocin da Tinubu zai naɗa.
Asali: Legit.ng