Zambar N525m: Kotun Daukaka Kara Ta Tabbatar Da Hukuncin Daurin Shekaru 235 Da Aka Yankewa Wani Dan damfara
- Kotun dauka kara ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 235 da aka yankewa wani matashi dan damfara
- Tun farko alkalin babbar kotun tarayya da ke Uyo, Agatha Okeke ne ya yankewa Mista Scales Olatunji hukuncin kan damfarar miliyan N525
- Mai shari'a na kotun daukaka kara, Justis Muhammed Idris ya kori karar da Olatunji ya daukaka sannan ya tabbatar da hukuncin kotun kasar
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
A ranar Juma'a, 2 ga watan Yuli, wata kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin da aka yankewa wani dan damfara ta intanet kan aikata zamba.
Agatha Okeke, allkalin babbar kotun tarayya da Uyo, ya yankewa Scales Olatunji hukunci a ranar 27 ga watan Yunin 2022 kan tuhumar da hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ke masa na aikata damfata ta intanet da zambar kudade.
Mai shari'a Okeke ya yanke masa hukuncin daurin shekaru 235 ba tare da tara ba
An yanke masa hukuncin daurin shekaru 235 a gidan yari ba tare da zabin biyan tara ba, jaridar Premium Times ta rahoto.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Hukumar EFCC reshen Uyo ce ta gurfanar da Mista Olatunji, kamar yadda hukumar yaki da rashawar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce:
"An hukunta mai laifin, bayan samun wani korafi daga ofishin yan sandan yankin Oslo, Norway, inda aka bukaci taimakon hukumar a binciken wani dan Najeriya, wanda ya damfari wasu yan Norway."
A cewar EFCC, Mista Olatunji dan wata kungiyar masu damfara ne wadanda suka shahara wajen kutse a sakonnin kasuwanci.
Mai laifin ya damfari gwamnatin Norway da yan kasar kudi da ya kai N525,172,580 sannan ya yi amfani da abun da ya samu daga laifin wajen siyan manyan kadarori a yankuna daban-daban a jihar Lagas.
Hukumar yaki da rashawar ta ce laifin ya yi karo da tanadin sashi na 18 (a) na dokar damfarar kudi (wanda aka haramta) kuma hukuncin laifin na karkashin na 15 (3) na wannan dokar.
Saboda rashin gamsuwa da hukuncin, mai laifin ya tunkari kotun daukaka kara, inda ya daukaka kara kan abubuwa 11 sannan ya roki kotun da ta soke hukuncin da kotun ta yanke masa.
Sabon hukuncin kotun daukaka kara
Da yake zartar da hukunci kan lamarin, kwamitin mutum uku na kotun daukaka kara karkashin jagorancin Justis Muhammed Idris, ya yi watsi da karar.
A cewarsa, lauyan masu kara ya tabbatar da shari'ar ba tare da wata shakka ba sannan ya amince da hukuncin kotun da ke kasa.
Dan Najeriya ya buga caca da N10, ya samu miliyan 2
A wani labari na daban, wani dan Najeriya mai suna @isthatUW a Twitter ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya wallafa takardar caca da ya buga, wanda ke nuna ya ci miliyan N2.
Abun da ya ba mutane mamaki shine cewa da N10 kacal ya buga wasanni fiye da 146,000. Sa'arsa ya sa mutane yi masa tambayoyi a sashinsa na sharhi.
Asali: Legit.ng