“Yunwa Nake Ji”: Direban Uber Wanda Ya Cinye Abincin Sallah Da Aka Ce Ya Kai Sako
- Wata yar Najeriya ta bayyana abun da ya wakana tsakanin kawarta da wani direban Uber da aka aika ya kai sakon abinci
- A cewar matashiyar, kawarta ta aiki matashin ya je ya karbo mata abincin Sallah daga wajen wata
- Sai dai kuma, direban Uber din wanda ya yi ikirarin cewa yana tsananin jin yunwa, ya cinye abincin sannan ya aike da sakon ban hakuri
Wata matashiya yar Najeriya mai suna @ozzyetomi ta je dandalin Twitter domin ba da labarin wani a al'amari mai ban mamaki da ya faru tsakanin wata da direban Uber.
Dirama ya barke bayan kawarta ta tura direban Uber ya karbo mata abincin Sallah daga wajen wata kawarta.
A cewar @ozzyetomi, direban Uber din ya gaggauta kawo karshen tafiyar tasa, sannan ya sace abincikin tare da tura sakon ban hakuri bayan ya cinye abincin.
Ozzy ta ba da labari:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Abun dariya kawata ta aika wani direban Uber ya je ya karbo mata abincin sallah daga wajen wata kawarmu, diraban Uber din ya kawo karshen tafiyan sannan ya sace abincin. Ya aika mata da sako cewa ta yi hakuri amma bai ci abinci bane tun safe."
Kawar ta aika sakon gargadi ga direban, tana mai barazanar kai karar shi da kuma sawa a sallame shi daga aiki.
Sakon ya ce:
"Za ka rasa aikinka na yan mintuna biyun nan. Shin darajarsa ya kai? Ka ji dadinka."
Da yake martani, direban ya amsa da sakon waya yana bayar da hakuri kan abun da ya aikata, cewa yana jin yunwa ne kuma bai ci komai ba tun safe.
"Yi hakuri ina ta jin yunwa ne ban ci komai ba tun safe shiyasa ina mai baki hakuri a kan haka," direban ya amsa."
Jama'a sun yi martani
@imoteda ta ce:
"“Awwwww mutum. Wannan abun bakin ciki ne."
@OparaBecky ta yi martani:
"Ta kai kararsa wajen Uber."
@Ox ta ce:
"Abun mamaki."
@mimi ojima ta ce:
"Ta neme shi sannan ta sa a kama shi, dam! Mugun mutum ne kuma barawo, na ji wani iri karanta wannan."
Matashiya ta koka bayan ta siya gwanjon N250k amma ta ga tarkace
A wani labarin kuma, wata matashiya ta shiga damuwa bayan ta siya sinkin gwanjo na N250k amma sai bata yi dace ba.
Matashiyar ta siya kayan yara ne amma sai ta tarar da tarkace a ciki wadanda basu da inganci.
Asali: Legit.ng