Musulunci Bai Yadda a Kashe Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi Ba, Malami

Musulunci Bai Yadda a Kashe Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi Ba, Malami

  • Wani fitaccen Malami ya maida raddi kan kisan da aka yi wa mahauci bisa zargin ɓatanci a jihar Sakkwato
  • Ustaz Adekilekun, ya ce mutane su taru su kashe wanda ya yi kalaman ɓatanci ba koyarwan addinin musulunci bane
  • A cewarsa mafi akasarin Kes din da ake samu a arewacin Najeriya kuma idan ka bincika zaka gano jahilci ne ya kawo

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Ustaz Abdul-Lateef Adekilekun, shugaban musulman ƙasar Yarbawa ya ce Addinin musulunci bai koyar da kashe wada ya yi kalaman ɓatanci ba.

Da yake zantawa da hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ranar Jumu'a a Ede, Adekilekun, ya bayyana addinin Musulunci da addinin zaman lafiya, babu tada zaune tsaye.

Waziri Abdul-Lateef Adekilekun.
Musulunci Bai Yadda a Kashe Wanda Ya Yi Batanci Ga Annabi Ba, Malami Hoto: thenationonline
Asali: UGC

Shehin Malamin ya yi wannan furucin ne domin maida martani kan abinda ya faru a jihar Sakkwato, inda mutane suka kashe Usman Buba bisa zargin ɓatanci.

Kara karanta wannan

Tsohon Gwamnan PDP a Arewa Ya Shiga Jerin Ministocin da Tinubu Zai Naɗa? Gaskiya Ta Bayyana

Jaridar The Nation ta ce a ranar Lahadi dandazon mutane suka yi ajalin Mahaucin bisa zargin ya yi kalaman ɓatanci ga fiyayyen halitta, Annabi Muhammad SAW.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wane hukunci Musulunci ya tanadarwa masu taɓa manzon Allah SAW?

Ustaz ɗin ya ƙara da cewa duk da haramun ne taɓa martabar Manzon Allah a musulunci amma akwai hanyoyin da Musulunci ya tanada wajen hukunta wanda ya yi ɓatanci.

Malam Adekilekun ya bayyana rashin ɗaukar matakin hukumomi da jahilci a matsayin abinda ke jawo mutane su ɗauki doka a hannu kan masu kalaman ɓatanci.

Ya kuma jaddada cewa akwai buƙatar wayar da kan Musulmai kan yadda ya dace su yi wa wanda ya yi kalaman ɓatanci.

A rahoton Vanguard, malamin ya ce:

"Na taɓa karanta wani littafi kuma an koya mun littafi shekara 61 da suka gabata, wanda ya rubuta littafin ya ce duk wanda ya zagi Manzon Allah a fille masa kai. Amma ba Aya babu Hadithi."

Kara karanta wannan

Wane Hukunci Aka Ɗauka Kan Kwamishinan Zaben Adamawa Hudu Ari? INEC Ta Fallasa Gaskiya

"Littafi ne kawai da wani masani ya rubuta, matsalar da muke fama da ita a Najeriya ita ce jahilci. A arewa ake fama da mafi akasarin masu yin kalaman ɓatanci kuma idan ka diba jahilci ne asalin sabab."
"Da wahala ka ji makamancin haka ta faru a kudancin Najeriya saboda ana wayar musu da kai sosai."

"Ku Ji Tsoron Allah" Malamai Sun Aike da Sako Ga Shugabannin Siyasa

A wani labarin na daban kuma Malamai da limaman jihar Ogun sun yi kira ga sabbin shugabanni su ji tsoron Allah wajen sauke nauyin amanar da ke kansu.

A cewar malaman ya kamata 'yan Najeriya su kwankwaɗi romon ayyuka da tsarukan da zasu tsamo su daga talauci sakamakon sadaukarwan da suka yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262