Babbar Sallah: Gwamna Adeleke Ya Tsallake Rijiya Da Baya’, Gwamnatin Jihar Osun Ta Yi Zargi
- An tattaro cewa Ademola Adeleke, gwamnan jihar Osun ya tsallake rijiya da baya a filin idi da ke Osogbo a ranar Laraba
- An tattaro cewa lamarin ya faru ne a lokacin sallar idi na babbar sallah wanda hakan ya sa gwamnan barin wajen
- A cikin wata sanarwa, Olawale Rasheed, kakakin gwamnan, ya bayyana cewa Adeleke ya bar filin idin bayan ya tsallake yunkurin kashe shi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Osogbo, Osun - Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ya yi kira da a kwantar da hankali bayan takaddaman da ya faru a filin idi na Osogbo a ranar Laraba, 28 ga watan Yuni.
A cewar BBC Pidgin, lamarin ya sa gwamnan barin filin idi da kin yin sallar idi tare da daukacin al'ummar Musulmi da suka taru.
Me yasa Ademola Adeleke ya bar masallaci a ranar idi
Wasu bidiyoyi sun yadu a soshiyal midiya inda suka nuno ana hayaniya a filin idin, sai dai kuma yawancin bidiyoyin basu yi bayanin abun da ya faru a wajen ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bayanai daban-daban sun fito dangane da lamarin da ya faru a filin idin, sannan rahotannin da suka fito daga ofishin gwamnan sun yi zargin cewa an yi yunkurin kashe Gwamna Adeleke ne.
Wani bangare na jawabin ya ce Gwamna Ademola Adeleke ya roki jama'a da su kwantar da hankali bayan ya tsallake yunkurin kashe shi a filin idin Osogbo.
Abun da Adeleke ya ce bayan barin filin idi
Wani bangare na sanarwar ta cewa:
"Gwamnatin ta kara kaduwa ne ganin yadda yan daba suka barbazu a fadin filin sallar idin da bayanan tsaro cewa an kwaso su ne domin su kashe Gwamnan da manyan jami'an gwamnati."
Olawale Rasheed, kakakin Adeleke, wanda ya sanya hannu a sanarwar, ya yi godiya ga Allah da ya kare gwamnan da tawagarsa sannan ya umurci jami'an tsaro da su kama wadanda ke da hannu a lamarin.
Sanarwar ta bayyana cewa an bukaci kwamishinan yan sandan jihar da ya tabbatar da ganin cewa masu laifin sun fuskanci doka duk matsayinsu a kasar.
Bam ya tashi da shugaban yan bindigar Zamfara, Dogo Gudali
A wani labari na daban, mun ji cewa hatsabibin shugaban yan bindiga da ya addabi al'ummar jihar Zamfara, Dogo Gudali, ya mutu.
Dogo Gudali ya hadu da ajalinsa ne sakamakon tashin bam da wasu mambobin kungiyarsa na ta'addanci suka dana.
Asali: Legit.ng